Ina Jin Daɗin Yadda Kiristoci Ke Bada Kyauta, Shan Ruwa Tare Da Musulmi, Shugaba Buhari

Ina Jin Daɗin Yadda Kiristoci Ke Bada Kyauta, Shan Ruwa Tare Da Musulmi, Shugaba Buhari

- Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari yace yana matukar farin ciki ganin yadda kiristoci ke shan ruwa tare da musulmi a lokacin azumin Ramadan

- Shugaban yace hakan na nuni da yadda addinan biyu ke son junan su da kuma yan uwantakar dake tsakaninsu

- Ya kuma taya yan Najeriya da musulmin duniya baki ɗaya barka da salla, da fatan Allah ya karɓi ibadunmu baki ɗaya

Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna matuƙar jin daɗinsa ganin yadda shagulgulan ƙaramar sallah yake nuna yan uwantaka, zaman lafiya da soyayya tsakanin kiristoci da musulmi.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Bindiga Sun Hallaka Ɗan Sanda a Wani Sabon Hari a Jihar Akwa Ibom

Shugaban yace ganin yadda kiristoci ke nuna kulawa ga yan uwansu musulmi a lokacin azumi ta hanyar shan ruwa tare da kuma basu kyaututtuka yana sashi farin ciki, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Shugaban ya bayyana haka ne a cikin sakon barka da sallah da ya fitar ta hannun mai magana da yawunsa, Garba Shehu, a Abuja ranar Laraba.

Ina Jin Daɗi Ganin Yadda Kiristoci Ke Bada Kyauta, Shan Ruwa Tare Da Musulmi, Shugaba Buhari
Ina Jin Daɗi Ganin Yadda Kiristoci Ke Bada Kyauta, Shan Ruwa Tare Da Musulmi, Shugaba Buhari Hoto: @GarShehu
Asali: Twitter

Shugaban ya ƙara da cewa abun farin ciki ne yadda kiristoci ke yiwa musulmai fatan alkairi, a wani lokacin ma su sha ruwa tare tare da basu kyauta a lokacin watan azumin Ramadana.

KARANTA ANAN: Mun Ƙwato Dala Miliyan $153M Daga Tsohuwar Ministan Man Fetur, Bawa

Shugaba Buhari yace: "Wannan na nuni da yadda suma musulmi suke taya yan uwansu kiristoci murna a lokacin shagul-gulan bikin addinin su."

"Aikata irin waɗannan abubuwa a tsakanin addinan yana ƙara danƙon zumunci, yan uwantaka da kuma yafewa juna."

Daga nan shugaba Buhari ya miƙa saƙon taya murna ga yan Najeriya da kuma dukkan musulmin duniya bisa zagayowar sallah ƙarama (Eidul Fitr) bayan kammala azumin watan Ramadana.

A saƙon da ya sakawa hannu, Buhari yace: "A wannan lokacin mai albarka, ina fatan shagalin sallah ƙarama (Eidul Fitr) ya kawo mana zaman lafiya, tsaro, aminci, da kuma yan uwaan taka tsakanin mu baki ɗaya."

A wani labarin kuma Mun San Inda Masu Satar Mutane Suke, Muna Tsoron Matsala ne Kawai, Lai Muhammed

Ministan yaɗa labarai da al'adu, Lai Muhammed yace bada jimawa ba yan Najeriya zasu ga sakamakon shirin da gwamnati keyi na kawo zaman lafiya a ƙasar nan.

Ministan yace magan-ganun da ake yaɗawa cewa gwamnati ta lulluɓe matsalar tsaron da ake fama da ita ba gaskiya bane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel