Mun Ƙwato Dala Miliyan $153M Daga Tsohuwar Ministan Man Fetur, Bawa

Mun Ƙwato Dala Miliyan $153M Daga Tsohuwar Ministan Man Fetur, Bawa

- Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa, yace sun sami nasarar kwato kimanin dala miliyan $153m daga hannun tsohuwar ministan man fetur

- Shugaban yace har yanzun suna gudanar da bincike a kan wasu tuhumomi da akewa Diezani Alison Madueke.

- Ya kuma ƙara jaddada maganarsa cewa a shirye yake yayi murabus daga kujerarsa matuƙar wani ya tursasa shi yayi abinda ba dai-dai ba

Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC, Abdulrasheed Bawa, yace hukumarsa ta dawo da dukiyar ƙasa kimanin dala miliyan $153m daga hannun tsohuwar ministan albarkatun man fetur, Diezani Alison Madueke.

KARANTA ANAN: Sama da Kashi 75% Na Yan Najeriya Basa Jin Daɗin Gwamnatin Buhari, Sanatan APC

Tun bayan fitar Diezani daga ofis a shekarar 2015 ta bar ƙasa Najeriya, ta koma Burtaniya da zama, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Bayan kuɗin da hukumar ta dawo dasu, an kuma ƙwato aƙalla kadarori 80 waɗanda aka yi ƙiyasin zasu kai darajar dala miliyan $80 daga hannun tsohuwar ministan kuma aka miƙa su ga gwamnatin tarayya.

Mun Ƙwato Dala Miliyan $153M Daga Tsohuwar Ministan Man Fetur, Bawa
Mun Ƙwato Dala Miliyan $153M Daga Tsohuwar Ministan Man Fetur, Bawa Hoto: @officialEFCC
Asali: Twitter

Bawa, wanda ya bayyana haka, yace a shirye yake yayi murabus daga muƙaminsa matuƙar wani daga cikin masu riƙe da madafun iko ya tursasashi yayi abinda ba dai-dai ba.

Shugaban ya ƙara da cewa babban ƙalubalen da suke fuskanta yanzun shine gurfanar da tsohuwar ministan a gaban shari'a kasancewar bata Najeriya.

Shugaban EFCC ɗin yace:

"Akwai zarge-zarge da yawa akan tsohuwar ministan, ina ɗaya daga cikin masu gudanar da bincike akan ta, kuma munyi aiki sosai. A ɗaya daga cikin tuhumar da ake mata, mun ƙwato tsabar kuɗi dala miliyan $153m."

KARANTA ANAN: Yan Bindiga na Buƙatar Tattaunawar Sulhu Da Malamai, Inji Tshohon Shugaban NHIS

"Sannan mun ƙwace kadarori 80 daga wajenta, waɗanda aka yi kiyasin zasu kai dala miliyan $80m. Sannan akwai wata tuhuma da ake mata ta dala miliyan $115m, ita ma muna cigaba da gudanar da bincike."

"Muna ƙoƙarin ganin wata ƙila ta dawo Najeriya, tabbas zamu sake duba abubuwan da ake tuhumarta sannan musan wane mataki zamu ɗauka na gaba."

Yayin da yake bada amsar tambayar da aka masa cewa ya zayyi idan wasu masu rike da madafun iko suka masa katsalandan a gudanar da aikinsa, Bawa yace:

"Matuƙar wani mutum yazo yasani inyi wani abu wanda ya saɓawa aiki na ko ya saɓawa abinda aka ƙirƙiri EFCC domin tayi, zan yi murabus daga kujerata."

A wani labarin kuma Rundunar Soji Ta Bayyana Matakin da Zata Ɗauka Kan Zargin da Ake Mata a Jihar Zamfara

Rundunar Sojin ƙasar nan ta bayyana matakin da zata ɗauka kan zargin da ake yiwa wani jami'inta na kisan wani mai siyar da kankana a jihar Zamfara.

Kakakin rundunar, Muhammed Yerima, yace tuni suka fara gudanar da bincike kan lamarin domin gano gaskiyar abinda ya faru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262