Father Mbaka Ya Yi Sabon Hasashe, Ya Bayyana Abinda Zai Faru Ga Gwamnatin Buhari Idan Aka Kai Masa Hari

Father Mbaka Ya Yi Sabon Hasashe, Ya Bayyana Abinda Zai Faru Ga Gwamnatin Buhari Idan Aka Kai Masa Hari

- Shahararren faston nan Father Mbaka ya gargadi gwamnatin da Buhari ke jagoranta game da kai masa hari

- Shugaban cocin na Katolika ya ce gwamnatin za ta fuskanci fushin Allah idan ta gwada yin hakan

- Father Mbaka ya kuma yi hasashen cewa akwai wani bala'i da ke tafe a Najeriya yayin da ya umarci gwamnati da ta samar da ayyukan yi ga matasa

Daraktan cocin Adoration Ministry, Enugu, Nigeria (AMEN), Fr Ejike Mbaka, ya ce bala'i yana ɓoye a Najeriya.

Ya kuma gargadi malamai a kasar nan da kada su mayar da kansu makamin bala'i ta hanyar shiga kowa don kare masu kashe talakawa.

Babban malamin na Katolika ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da jawabinsa na ranar lahadi a cikin faifan bidiyo da ya yadu a yanar gizo.

Father Mbaka Ya Saki Sabon Wahayi, Ya Bayyana Abinda Zai Faru Ga Gwamnatin Buhari Idan Aka Kai Masa Hari
Father Mbaka Ya Saki Sabon Wahayi, Ya Bayyana Abinda Zai Faru Ga Gwamnatin Buhari Idan Aka Kai Masa Hari Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Isa Pantami Ya Tsawaita Wa’adin Hade NIN-SIM Har Zuwa 30 Ga Watan Yuni

Mbaka ya ci gaba da cewa babu wata katanga da za a yi wa Majalisar Dokoki da tsaro a fadar Aso Rock Villa da zai kare kasar nan “idan ba su kula da matasa tare da basu ayyukan yi ba, da magance duk wadannan matsalolin da Ruhu Mai Tsarki ya gabatar a ranar Laraba .”

Mbaka ya gargadi gwamnatin Buhari cewa shi (Mbaka) zai zama mutum na ƙarshe da za su yi yaƙi da shi, inda ya ƙara da cewa fushin Ubangiji zai sauka a kansu idan sun gwada hakan jaridar Punch ta ruwaito.

Ya ce, “Mutum na karshe da wannan gwamnatin za ta yi fada da shi shine Father Mbaka saboda idan suka aibata ni, fushin Allah zai kasance a kansu kuma yadda za su kare zai girgiza kowa.

“Ina wakiltar talakawa ne, masu karamin karfi. Ina wakiltar wadanda ba kowan kowa ba; Ina wakiltar marasa aikin yi, ina wakiltar majiyyata, ina wakiltar wadanda aka cuta. Duk wadanda aka wulakanta a kasar nan, ni ne ubansu.

"Don haka, lokacin da yarana ke kuka ba zan iya yin shiru ba," in ji shi, yana mai cewa "wannan ba shi ne karo na farko da zai yi magana a kan mummunan shugabanci na wannan gwamnatin ba."

Shehin malamin ya bayyana cewa Fadar Shugaban kasa na kai masa hari ne saboda ya sanya wa Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar 'yan asalin yankin Biafra albarka.

KU KARANTA KUMA: Yan Boko Haram sun kutsa garinsu Zulum, sun sheƙe rayuka 7, sun kone gidaje

“Idan sun damu cewa ina sanya wa Nnamdi Kanu albarka, a duk inda yake, Allah yana sanya masa albarka. Yana numfashi; cewa yana bacci ya farka, shin wannan ba albarka bane? Ko shi ba dan uwana bane? A ruhaniya, shi ba ɗana bane? To menene matsalar su? Sun shagalta da sanya wa mutane da garuruwa suna da yan ta'adda.

“Idan abin da ke faruwa a Kaduna, Kano, Nasarawa, Maiduguri, Benue, Niger; idan duk wadannan wurare an sanya masu sunan jihohin 'yan ta'adda, shin ba za a bayyana Najeriya gaba daya a matsayin kasar ta'addanci ba? Idan wani ya faɗi gaskiya, mutumin ya zama ɗan ta’adda,” in ji shi.

“Ya kamata su kiyaye saboda rashin tsaro da nake magana a kai na iya shafar su. Ko Shehu Garba da yake magana, ‘yan fashin na iya zuwa su kashe shi,” ya kara da cewa.

A gefe guda, limamin babban cocin Adoration Ministry da ke garin Enugu, Rabaren Ejike Mbaka, ya tanka fadar shugaban kasar Najeriya a kan zargin da ta ke yi masa.

Ejike Mbaka ya bayyana cewa akwai yarinta a cikin zargin da ake yi masa, ya ce lamarin abin dariya ne, jaridar Vanguard ce ta fitar da wannan rahoto a jiya.

Babban Faston ya musanya abin da Garba Shehu yake fada na cewa ya na sukar shugaba Muhammadu Buhari ne saboda an hana shi wasu kwangiloli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel