Neman kwangila: Abin da ya kai ni wajen Buhari tare da mutum 3 – Mbaka ya yi magana

Neman kwangila: Abin da ya kai ni wajen Buhari tare da mutum 3 – Mbaka ya yi magana

Limamin babban cocin Adoration Ministry da ke garin Enugu, Rabaren Ejike Mbaka, ya tanka fadar shugaban kasar Najeriya a kan zargin da ta ke yi masa.

Ejike Mbaka ya bayyana cewa akwai yarinta a cikin zargin da ake yi masa, ya ce lamarin abin dariya ne, jaridar Vanguard ce ta fitar da wannan rahoto a jiya.

Babban Faston ya musanya abin da Garba Shehu yake fada na cewa ya na sukar shugaba Muhammadu Buhari ne saboda an hana shi wasu kwangiloli.

Faston ya yi wannan martani ne a lokacin da yake huduba a ranar Lahadi, 2 ga watan Mayu, 2021.

KU KARANTA: Mbaka ya bukaci kwangila, aka han shi - Garba Shehu

Idan su na maganar ba Mbaka kwangiloli, abin dariya yake ba ni, akwai yarinta a zargin da ake jifa na da shi.” Mbaka ya ce: “Ba na so in yi magana kan lamarin.”

“Duk mai fadan wannan, abin kunya ne shi da wadanda yake wakilta.” Mbaka yake cewa shi Malami ne, ya fi karfin ‘Dan Adam ya kalubalanci abin da yake fada.

Na yi shiru ne saboda ina jiran su tuba, har sai lokacin da Ubangiji ya ce in maida martani.”

Ya ce: “Duk mai ja da sako ne, ya na kalubalantar Ubangijin tsawo ne, saboda haka ya yi hattara. Mbaka ba limami ba ne kurum, mutum ne mai sama wa jama’a aiki.”

KU KARANTA: APC Za Ta Kai Ƙarar Mbaka Wurin Fafaroma

Neman kwangila: Abin da ya kai ni wajen Buhari tare da mutum 3 – Mbaka ya yi magana
Ejika Mbaka da Shugaba Buhari
Asali: UGC

Mbaka ya nuna ya fi karfin maula, ya je maula: “Da yardar Ubangiji kuma wadanda su ke cin abinci ta karkashi na a kowane watan Duniya, sun haura mutane 23, 000.”

“Ban zo nan domin in kare kai na ba, amma mutane uku da ya ambata, mutane ne da su ka yi ikirarin za su iya magance matsalar rashin tsaro.” Inji Rabaren Mbaka.

“An yi wannan ne a wa’adin shugaban kasa na farko (lokacin Abba Kyari), wadannan mutane sun fada masu za su iya kawo karshen rashin tsaro ne a cikin wata daya.”

Mbaka ya ce ya hada wadannan mutane da gwamnati ne kurum, amma ba shi ya nemi alfarma ba. Limamin ya kuma ce wadanda ake ba kwangila ba su fi shi komai ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel