Yanzu Yanzu: Isa Pantami Ya Tsawaita Wa’adin Hade NIN-SIM Har Zuwa 30 Ga Watan Yuni

Yanzu Yanzu: Isa Pantami Ya Tsawaita Wa’adin Hade NIN-SIM Har Zuwa 30 Ga Watan Yuni

- Sheikh Isa Pantami, ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin zamani ya ce an kara wa'adin hade layukan SIM da lambar shedar dan kasa

- An tsawaita wa'adin shirin ne zuwa ranar 30 ga watan Yuni, 2021

- Hakan na kunshe a cikin wata sanarwa daga daraktan hulda da jama’a na hukumar sadarwa ta Najeriya da kuma Shugaban Hukumar Kula da Shaidun Dan Kasa

Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin zamani na Kasa, Isa Pantami, ya tsawaita wa’adin hade lambar shedar dan kasa da layukan waya.

An tsawaita wa'adin shirin har zuwa ranar 30 ga watan Yuni, 2021.

KU KARANTA KUMA: Sai an lale mana N100m za mu fito da Shugaban karamar hukumar Kogi inji ‘Yan bindiga

Yanzu Yanzu: Isa Pantami Ya Tsawaita Wa’adin Hade NIN-SIM Har Zuwa 30 Ga Watan Yuni
Yanzu Yanzu: Isa Pantami Ya Tsawaita Wa’adin Hade NIN-SIM Har Zuwa 30 Ga Watan Yuni Hoto: @DrIsaPantami
Asali: Twitter

Punch ta ruwaito cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun hadin gwiwar daraktan hulda da jama’a na hukumar sadarwa ta Najeriya, Ikechukwu Adinde; da kuma Shugaban Hukumar Kula da Shaidun Dan Kasa, Kayode Adegoke.

An kuma tattaro cewa Pantami, wanda ya sha suka kan kalamansa na baya kan kungiyar Taliban, ya bayyana cewa an hada katunan SIM miliyan 54 da NIN.

A wani labarin, mun ji a baya cewa Hukumar Kula da Sadarwa ta Najeriya ta ce ba za ta katse masu amfani da layin sadarwar ba sakamakon ci gaba da alakanta lambobin shedar kasa (NINs) da katinan SIM.

Daily Trust ta ruwaito cewa NCC a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, 6 ga Janairu, ta ce bayanin ya zama dole don kawar da tsoron masu amfani da layuka da sauran jama’a.

KU KARANTA KUMA: Mawaki ya rangadawa Ministan Buhari wakar batanci saboda ya fito ya tona masa asiri

An ruwaito mai magana da yawun hukumar, Ikechukwu Adinde yana cewa wani binciken da aka gudanar kwanan nan akwai kusan katinan SIM guda hudu zuwa biyar ga kowane dan Najeriya mai amfani da waya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng