Yan Boko Haram sun kutsa garinsu Zulum, sun sheƙe rayuka 7, sun kone gidaje

Yan Boko Haram sun kutsa garinsu Zulum, sun sheƙe rayuka 7, sun kone gidaje

- Mayakan ta'addanci na Boko Haram sun halaka farar hula shida tare da jami'in tsaro a garin Ajari dake karamar hukumar Mafa

- Sun kai mugun harin ne a daren Litinin wurin karfe 1 na dare inda suka dinga kone gidajen jama'a a garin mai nisan kilomita 30 zuwa Maiduguri

- Mukaddashin gwamnan jihar, Usman Kadafur, ya bada umarnin gaggauta gyara gidajen da aka kone tare da bada tabbacin za a tsananta tsaron jihar

Farar hula shida tare da jami'in tsaro daya ne suka rasa rayukansu yayin da mayakan Boko Haram suka kai farmaki garin Ajari dake karamar hukumar Mafa ta jihar Borno a ranar Litinin.

Karamar hukumar Mafa ce inda Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum ya fito.

Kamar yadda sakataren karamar hukumar, Mohammed Sherrif, yace, "'Yan ta'addan sun tsinkayi garin wurin karfe 1 na dare kuma suka dinga bankawa gidajen jama'a wuta sannan suka kashe farar hula shida da wani jami'in tsaro daya."

Mafa tana da nisan kusan kilomita 30 daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno, jaridar The Punch ta ruwaito.

KU KARANTA: Shigar Boko Haram Abuja: 'Yan sandan FCT sun magantu, an fara sintiri babu kakkautawa

Yan Boko Haram sun kutsa garinsu Zulum, sun sheƙe rai 6, sun kone gidaje
Yan Boko Haram sun kutsa garinsu Zulum, sun sheƙe rai 6, sun kone gidaje. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kayatattun Hotunan katafaren filin jiragen sama na China ya bar mutane baki bude

Harin yana zuwa ne bayan watanni masu yawa da aka samu zaman lafiya a karamar hukumar.

Mukaddashin gwamnan jihar, Usman Kadafur, ya bada umarnin gaggauta gyara gidajen da suka kone yayin da yake tabbatarwa da mazauna yankin cewa gwamnati za ta yi iyakar kokarinta wurin tabbatar da tsaro a jihar.

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Ebonyi a ranar Lahadi ta kama wasu harsasai 753 na wata muguwar bindiga GPMG a jihar.

An boye harsasan a wani buhu wanda aka saka a wata motar haya daga garin Abakaliki, za a kaisu garin Umuahi na jihar Abia, Daily Trust ta ruwaito.

Wannan na zuwa ne yayin da hare-hare suka tsananta a kan jami'an tsaron dake yankin kudu maso gabas da kuma kudu kudu na kasar nan. 'Yan bindigan da ake zargin mambobi ne na kungiyar IPOB ake zargi da wadannan hare-haren.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel