Dr Bashir Aliyu Umar: Abubuwa 10 Ga Mai Son Dacewa da Lailatul Qadari

Dr Bashir Aliyu Umar: Abubuwa 10 Ga Mai Son Dacewa da Lailatul Qadari

Tsokacin Edita: Watan Ramadana, watan da Allah ya saukar da Al-Kur'ani mai girma wata ne mai falala daga cikin watannin musulunci. A watan Ramadana ne Allah ya kebe ibadar Azumi, wacce ya ce shi ke ba da lada gareta na musamman.

Hakazalika, a watan Ramadana Allah ya kebe wani dare mai daraja, wato daren Lailatul Qadari. Kur'ani ya siffanta daren da kwatankwacin dare 1000.

Daren Lailatul Qadari na zuwa ne cikin goman karshe na watan Ramadana. Hakan yasa hadisai da dama ke magana kan a yawaita ibada da tsayuwar salloli cikin dare domin dacewa da daren Lailatul Qadari.

KU KARANTA: Don Allah, Ku Hanzarta Kai Rahotona Ga Paparoma, Mbaka Ya Kalubalanci Barazanar APC

Dr Bashir Aliyu Umar: Abubuwa 10 ga mai son dacewa da Lailatul Qadari
Dr Bashir Aliyu Umar: Abubuwa 10 ga mai son dacewa da Lailatul Qadari Hoto: lightofislam.com.ng
Asali: UGC

Dr Bashir Aliyu Umar, limamin masallacin Al-Furqan da ke birnin Kano, ya lissafa wasu abubuwa guda 10 da ya ce su ne jagoran mai neman dacewa da daren Lailatul Qadari, kamar haka:

1. Niyyar neman yardar Ubangiji

2. Neman gafara ga Ubangiji kasancewar samun rabauta ya ta'allaka ne ga irin afuwar da Allah ya yi wa dan adam a wannan dare.

3. Wankan tsarki tsakanin Magriba da Isha'i ko kuma bayan Isha'i kamar yadda ya zo a sunnar Annabi Muhammad (SAW). Har wa yau, yana da kyau a sanya tufafi mai kyau domin daren tamkar Idi ne.

4. Tashin iyali domin neman rabauta kamar yadda ya zo a sunnah cewa Annabi SAW duk dare yana tashin iyalansa domin yin ibada.

5. Raya kowanne dare da sallah da sauran ibadu daidai gwargwado ba tare da yin barcin da ya wuce kima ba. Saboda ana son mutum ya kaurace wa makwancinsa a wadannan darare.

KU KARANTA: Sojoji Sun Dakile Harin 'Yan Boko Haram Na Mamaye Garin Kala-Balge a Jihar Borno

6. Mutum ya guji rigima ko musu ko da kuwa da iyalinsa ne domin musu da jayayya na janyo daukewar rahama.

7. Yawan yin addu'ar da Annabi ya koya wa matarsa, Aisha wato Allahumma Innaka Afuwun Tuhibbul Afwa Faafu anna.

8. Mutum ya kyautata wa mahaifansa a dukkan dararen goman karshe, abin da zai sa su yi farin ciki da mutum.

9. A kuma yawaita addu'ar neman 'yantawa daga wutar jahannama.

10. Sannan a yi tawassuli da dararen goma wajen neman Allah ya fitar da Musulmi daga sharrin annobar korona.

KU KARANTA: Jirgin Kasa Da Ya Taso Daga Legas Zuwa Zariya Ya Yi Hatsari a Jihar Kaduna

A gefe guda, Ahmad Gumi, fitaccen malamin addinin Islama, ya ce al’ummar kasar za su yi nadama idan aka tsige Isa Pantami, ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani daga mukaminsa, TheCable ta ruwaito.

Yawancin 'yan Najeriya da kungiyoyi suna ta rokon Shugaba Muhammadu Buhari ya tsige Pantami bayan bidiyo da aka nuna a shekarun 2000 sun sake bayyana inda aka ga ministan yana goyon bayan Al-Qaeda da Taliban.

Pantami, duk da haka, ya sake tunani game da tunaninsa na baya-bayan nan game da kungiyoyin ta'addancin, yana mai cewa matsayinsa a lokacin ya dogara ne da fahimtarsa lokacin da yake saurayi.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel