Za Ku Yi Matukar Nadama Idan Aka Sauke Dr Pantami, Gumi Ga ’Yan Najeriya

Za Ku Yi Matukar Nadama Idan Aka Sauke Dr Pantami, Gumi Ga ’Yan Najeriya

- Sheikh Gumi, fitattacen malamin addinin Islama ya bayyana ra'ayinsa kan minista Pantami

- Malamin ya bayyana cewa, idan aka tube Pantami, 'yan Najeriya zasu yi matukar dana-sani

- Ya ce Pantami ba dan ta'adda bane, bai taba kashe wani ba ko ba da umarnin kashe wani a kasar

Ahmad Gumi, fitaccen malamin addinin Islama, ya ce al’ummar kasar za su yi nadama idan aka tsige Isa Pantami, ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani daga mukaminsa, TheCable ta ruwaito.

Yawancin 'yan Najeriya da kungiyoyi suna ta rokon Shugaba Muhammadu Buhari ya tsige Pantami bayan bidiyo da aka nuna a shekarun 2000 sun sake bayyana inda aka ga ministan yana goyon bayan Al-Qaeda da Taliban.

Pantami, duk da haka, ya sake tunani game da tunaninsa na baya-bayan nan game da kungiyoyin ta'addancin, yana mai cewa matsayinsa a lokacin ya dogara ne da fahimtarsa lokacin da yake saurayi.

KU KARANTA: Saura Kiris ’Yan Boko Haram Su Shiga Babban Birnin Tarayya Abuja, in ji Gwamnan Neja

Za ku yi matukar nadama idan aka sauke Dr Pantami, in ji Gumi
Za ku yi matukar nadama idan aka sauke Dr Pantami, in ji Gumi Hoto: premiumtimesng.com
Asali: Facebook

A wata hira da gidan talabijin na Roots a ranar Litinin, Gumi ya ce zargin da ake yi wa ministan bashi da tushe kuma ya kamata a yi watsi da shi.

“Ba za ku iya musuluntar da duk duniya ba. Yesu Kiristi ya zo; bai iya mai da duk duniya kirista ba. Babu wanda zai musuluntar ko kuma ya mai da Najeriya kirista,” in ji Gumi.

“Duk ayyukansa, dari bisa dari, sun nuna shi ba dan ta’adda bane. Wadanda suke 'yan ta'adda suna bibiyar rayuwarsa. Ya kamata Ministan ya ci gaba. Kasancewarsa a can yana yakar akidar ta'addanci.

“Ku nuna min mutum daya da ya kashe. Bai kashe kowa ba. Bai ba da umarnin a kashe kowa ba. Ku yi watsi da labaran karya.

"Yana daidaita gwamnati a tsakanin wani bangare na matasa, wanda muke so su zo su shiga aikin gina kasa. Bai kamata a jefar dashi ba. A bar shi. Shi ba mai goyon bayan 'yan ta'adda bane.

“Kuma ku kuna yakarsu. A'a, ya kamata ku kara samun mutane kamar Pantami ku basu iko. Zai daidaita lamurra. Kar ku cire shi. Zaku yi nadama."

Fadar shugaban kasar ta kuma kare Pantami, inda ta yi zargin cewa kamfanonin yada labarai da sadarwa (ICT) su ne ke kitsa kullin a tsige ministan.

KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun Hallaka Wani DPO da Jami’ansa 8 a Wata Jihar Arewacin Najeriya

A wani labarin, Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo a ranar Lahadi ya ce "akwai alkawarin Allah" ga Najeriya kuma kasar za ta zama "gidan zaman lafiya, tsaro da ci gaba irin wanda ba a taba ganin irinsa ba a wannan nahiya da ma ta gaba da ita."

Ya yi wannan bayanin ne lokacin da yake jawabi a wajen babban taron shekara-shekara karo na 108 na Babban Taron Baptist na Najeriya a Jihar Ogun, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Farfesa Osinbajo ya kara da cewa Najeriya "za ta kasance cibiyar ci gaban tattalin arziki da kimiyya na karni na 21," a cewar wata sanarwa da mai magana da yawunsa Laolu Akande ya sanya hannu akai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel