Don Allah, Ku Hanzarta Kai Rahotona Ga Paparoma, Mbaka Ya Kalubalanci Barazanar APC

Don Allah, Ku Hanzarta Kai Rahotona Ga Paparoma, Mbaka Ya Kalubalanci Barazanar APC

- Babban malamin darikar Katolika ya mai da martani ga jam'iyyar APC kan barazanar kai rahotonsa Rum

- Malamin ya bayyana cewa, idan Paparoma ya ji labarin aikin da ya aikata sai dai ma ya yaba masa, ya tafa masa

- Hakazalika ya bayyana cewa, shi ba son matsayi yake ba, shi yasa bai son APC ta kai rahotonsa ga Paparoma

Babban malamin darikar Katolika Fr Ejike Mbaka ya bukaci jam’iyyar APC, da kada ta bata lokaci wajen aiwatar da barazanar da ta ke yi na kai rahotonsa ga Paparoma, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Mbaka na mayar da martani ne ga Yekini Nabena, Mataimakin Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar APC wanda a cikin wata sanarwa ya ke kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ko dai ya sauka ko kuma a tsige shi saboda kalubalen da ake fuskanta a yanzu rashin tsoron Allah ne.

Mbaka ya yi magana ne game da barazanar tare da wasu batutuwa da ya gabatar a makon da ya gabata yayin hudubarsa a ranar Lahadi.

KU KARANTA: Jirgin Kasa Da Ya Taso Daga Legas Zuwa Zariya Ya Yi Hatsari a Jihar Kaduna

Don Allah, Ku Hanzarta Kai Rahotona Ga Paparoma, Mbaka Ya Kalubalanci Barazanar APC
Don Allah, Ku Hanzarta Kai Rahotona Ga Paparoma, Mbaka Ya Kalubalanci Barazanar APC Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Da yake watsi da barazanar kai rahotonsa ga Paparoma, Mbaka ya bukaci jam’iyyar ta APC da ta yi hakan cikin gaggawa, yana mai cewa, “Idan Paparoma ya san ina magana ne a kan rashin shugabanci mai kyau, zai tafa min. Don haka don Allah, da sauri ku tafi Rum.

"Abin da ya sa ba na ma son su tafi Rum shi ne saboda, idan Rome ta ji wannan batu, za su iya ba ni wani matsayi da ba na so."

KU KARANTA: Sojoji Sun Dakile Harin 'Yan Boko Haram Na Mamaye Garin Kala-Balge a Jihar Borno

A wani labarin, Ejike Mbaka ya bayyana cewa akwai yarinta a cikin zargin da ake yi masa, ya ce lamarin abin dariya ne, jaridar Vanguard ce ta fitar da wannan rahoto a jiya.

Babban Faston ya musanya abin da Garba Shehu yake fada na cewa ya na sukar shugaba Muhammadu Buhari ne saboda an hana shi wasu kwangiloli.

Faston ya yi wannan martani ne a lokacin da yake huduba a ranar Lahadi, 2 ga watan Mayu, 2021.

Asali: Legit.ng

Online view pixel