Sojoji Sun Dakile Harin 'Yan Boko Haram Na Mamaye Garin Kala-Balge a Jihar Borno

Sojoji Sun Dakile Harin 'Yan Boko Haram Na Mamaye Garin Kala-Balge a Jihar Borno

- 'Yan ta'addan Boko Haram sun kai hari garin Rann, hwdkwatar garin Kala-Balge a jihar Borno

- Sojojin Najeriya sun samu nasarar dakile harin, sun kuma hana 'yan ta'addan shiga garin na Rann

- Wasu mutane biyar sun ji raunuka, yayin da wata mata ta rasa ranta a asibiti sakamakon harbin bindiga

Akalla mutum daya farar hula ya rasa ransa yayin da wasu biyar suka jikkata lokacin da wasu da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne suka yi yunkurin kutsawa cikin garin Rann, hedkwatar karamar hukumar Kala-Balge da ke jihar Borno, in ji majiyar tsaro.

Lamarin ya faru ne lokacin da haramtacciyar kungiyar ta mamaye garin Rann da misalin karfe 6:15 na maraice suna harbe-harbe amma suka gamu da turjiya daga sojojin Najeriya.

Wata majiyar tsaro ta tabbatar da cewa sojoji sun yi amfani da bindigoginsu a yayin harin da aka kai lamarin da ya haifar da sakamakon lalata motar bindigogi ta maharan, Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: Jirgin Kasa Da Ya Taso Daga Legas Zuwa Zariya Ya Yi Hatsari a Jihar Kaduna

Sojoji Sun Dakile Harin 'Yan Boko Haram Na Mamaye Garin Kala-Balge a Jihar Borno
Sojoji Sun Dakile Harin 'Yan Boko Haram Na Mamaye Garin Kala-Balge a Jihar Borno Hoto: dw.com
Asali: UGC

Majiyar ta ce mutane biyar, ciki har da ‘yan kungiyar hadin gwiwa ta farin kaya (JTF) sun samu rauni a harin.

“Wata farar hula (wata baiwar Allah) daga baya ta mutu sakamakon harbin bindiga da ya same ta a cinyarta. A yayin harin, mutane biyar sun ji rauni sakamakon harbi da bindiga kuma yanzu haka suna ci gaba da karbar magani a sansanin sojoji.

”Sojoji ba su bar maharan sun shigo garin ba, sun fara fatattakarsu a bakin kofa. Wannan gagarumin aiki ne ga sojoji a Rann.” Inji majiyar.

KU KARANTA: Likitan Da Ya Bayyana Maboyar Osama Bin Laden Na Neman Gwamnati ta Sake Shi

A wani labarin, Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun hallaka kwamishinan hukumar fansho na jihar Kogi, Solomon Akeweje, jaridar Punch ta ruwaito.

An rahoto cewa an kashe shi ne da yammacin ranar Asabar yayin da yake dawowa daga Ilorin zuwa Kabba.

An ce 'yan bindigan sun harbi motarsa a Eruku, tazarar kilomita kadan daga Egbe a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel