Ku Magance Matsalar Tsaron Jami’o’i Cikin Gaggawa, ASUU Ta Gargaɗi FG

Ku Magance Matsalar Tsaron Jami’o’i Cikin Gaggawa, ASUU Ta Gargaɗi FG

- Ƙungiyar malaman jami'oi ASUU, reshen jami'ar koyon aikin gona dake Makurdi FUAM, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da dukkan hukumomin tsaro na ƙasa su magance matsalar tsaro a makarantun jami'a

- Har ila yau ASUU-FUAM tayi Allah wadai da harin da wasu yan bindiga suka kai makarantar koyon aikin gona FUAM

- Ƙungiyar tace ya kamata ayi gaggawar daƙile wannan matsalar, domin waɗannan mutanen burinsu su mamaye ƙasar nan

Ƙungiyar malaman jami'o'i ASUU, reshen jami'ar koyon aikin gona, Makurɗi (FUAM) ta kira yi gwamnatin tarayya da ta gaggauta ceto jami'o'in ƙasar nan daga ayyukan yan ta'adda.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: An tsaurara matakan tsaro a zauren majalisa saboda barazanar tsaro

Shugaban ASUU-FUAM, Dr Simon Ejembi, yace kiran ya zama wajibi biyo bayan ƙaruwar matsalar tsaro a ƙasar nan, kamar yadda jaridar Dailytrust ta ruwaito.

A yan kwanakin baya ne wasu yan bindiga suka sace wasu ɗaliban jami'ar FUAM a ɗakin da ake gudanar da lakca suna tsakiyar karatu.

Ku Magance Matsalar Tsaron Jami’o’i Cikin Gaggawa, ASUU Ta Gargaɗi FG
Ku Magance Matsalar Tsaron Jami’o’i Cikin Gaggawa, ASUU Ta Gargaɗi FG Hoto: schoolings.org
Asali: UGC

Ejembi yace faruwar lamarin yasa makarantar ta shiga cikin jerin makarantu da sakandire da yan bindiga suka kai hari kwanan nan.

KARANTA ANAN: Gwamnatin Bauchi ta dakatar da wani malamin addinin musulunci Daga gudanar da Wa'azi

A jawabin shugaban ASUU-FUAM yace:

"ASUU-FUAM tayi Allah wadai da harin da aka kaima ɗaliban mu har aka sace wasu daga cikinsu kuma muna kira ga hukumomin tsaro da su tabbata sun kamo waɗanda suka aikata wannan aikin domin a hukunta su yadda doka ta tanadar."

"Mu, (ASUU-FUAM), muna kira ga masu riƙe da madafun iko da dukkan hukumomin tsaro da su ceto ƙasar nan daga mamayewar da wasu makiyanta ke kokarin yiwa cigaban ƙasar nan tamu da kuma ƙoƙarin ƙarɓe mulkin ƙasar da suke yi."

A wani labarin kuma Sakataren Amurka yayi magana kan matsalar tsaro bayan ganawarsa da Shugaba Buhari

Sakataren ƙasar Amurka, Antony Blinken, yayi magana kan matsalar tsaron Najeriya a karon farko tun bayan ganawarsa da shugaban ƙasa Buhari.

Yace ƙalubalen tsaron da Najeriya ke fama dashi na musamman ne, amma ƙasar sa a shirye take ta taimkawa Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel