Gwamnatin Bauchi ta dakatar da wani malamin addinin musulunci Daga gudanar da Wa'azi

Gwamnatin Bauchi ta dakatar da wani malamin addinin musulunci Daga gudanar da Wa'azi

- Gwamnatin jihar Bauchi ta dakatar da wani malamin addinin musulunci daga gudanar da wa'azi a fadin jihar

- Gwamnatin tace ta gano malamin na caccakar sahabban Manzon Allah (SAW) wanda hakan ka iya harzuƙa mutanen jihar

- Ta ce ta yanke wannan hukuncin na dakatarwan ne domin tabbatar da zaman lafiyar a jihar

Gwamnatin jihar Bauchi ta dakatar da wani malamin addinin musulunci daga gudanar da wa'azi har sai baba-ta-gani saboda zargin wuce gona da iri a karatunsa.

KARANTA ANAN: Sakataren Amurka yayi magana kan matsalar tsaro bayan ganawarsa da Shugaba Buhari

Dakatarwan na ƙunshe ne a wata wasiƙa da kwamishinan al'amuran addini na jihar, Ahmad Jalam, ya sakawa hannu.

A jikin wasiƙar an saka adireshin Malam Abubakar Idris, Azare, ƙaramar hukumar Katagum , jihar Bauchi.

Gwamnatin Bauchi ta dakatar da wani malamin addinin musulunci Daga gudanar da Wa'azi
Gwamnatin Bauchi ta dakatar da wani malamin addinin musulunci Daga gudanar da Wa'azi Hoto: Labari daga Bauchi FB Fage
Asali: Facebook

A wasiƙar wadda akai wa take da: "Karya doka da rashin ɗa'a ga dokar wa'azi a jihar Bauchi" an gano malamin na caccakar sahabban Annabi Muhammad (SAW) a cikin wa'azinsa.

Gwamnatin tace kalaman malamin ka iya jawo ruɗani tsakanin jama'a kuma zai iya sa mutane su karya doka a faɗin jihar.

Bisa wannan dalilin ne gwamnati ta dakatar dashi gudanar da wa'azi a faɗin jihar.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Ƙasar Amurka Ta Bayyana Matsayin Najeriya A Wajenta

Wasiƙar tace:

"Gwamnatin jihar Bauchi ta gano wasu kalamanka da wa'azin ka, rahoto ya nuna cewa kana batanci ga sahabban Annabi Muhammad SAW a cikin wa'azinka."

"Wannan a bayyane yake, ɗabi'ar yin hakan ya saɓa ma dokokin wa'azi a jihar mu, kalamanka ka iya harzuƙa mutane kuma hakan na iya jawo rikici, gwamnati ba zata amince da haka ba."

"Saboda waɗannan dalilai, mun dakatar da kai daga gudanar da wa'azi da kuma jagorantar sallar jumu'a domin tabbatar da zaman lafiya a faɗin jihar mu."

A wani labarin kuma Gwamnatin Kaduna ta bayyana dalilin da yasa yan bindiga suka dirar ma Jihar da ta'addanci

Gwamnatin jihar Kaduna ta yi Allah wadai da kisan da yan bindiga keyiwa ɗalibai masu karatu a makarantun gaba da sakandire na Jihar.

Gwamnatin tace yan bindigar na haka ne don kawai su jawo hankalinta ta canza matsayarta na 'Ba biyan kuɗin fansa' da kuma 'Ba maganar sulhu da yan bindiga'

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel