Sakataren Amurka yayi magana kan matsalar tsaro bayan ganawarsa da Shugaba Buhari

Sakataren Amurka yayi magana kan matsalar tsaro bayan ganawarsa da Shugaba Buhari

- Sakataren ƙasar Amurka, Antony Blinken, yayi magana kan matsalar tsaron Najeriya a karon farko tun bayan ganawarsa da shugaban ƙasa Buhari

- Yace ƙalubalen tsaron da Najeriya ke fama dashi na musamman ne, amma ƙasar sa a shirye take ta taimkawa Najeriya

- Sakataren wanda ya bayyana haka yayin da yake amsa tambayoyi daga wajen yan jaridar Kenya da Najeriya, yace za'a fara magance tushen matsalolin

Sakataren ƙasar Amurka, Antony Blinken, ya bayyana matsalar tsaron da Najeriya ke fama dashi da "Na musamman" kamar yadda Punch ta ruwaito.

Sakataren ya bayyana hakane yayin tattaunawarsa da yan jaridar kasar Kenya da kuma na Najeriya.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Ƙasar Amurka Ta Bayyana Matsayin Najeriya A Wajenta

Blinken, wanda ya bada amsar tambayar da aka masa cewa taya ƙasar Amurka zata taimakawa Najeriya wajen magance matsalar tsaron da take fama dashi na mayaƙan Boko Haram, yan bindiga da kuma IPOB.

Yace: "Zan iya cewa ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta a ɓangaren tsaro na musamman ne, ko ya kuke kiransu dashi; ta'addanci, yan bindiga, dukkan su dai ƙalubale ne na musamman."

Sakataren Amurka yayi magana kan matsalar tsaro bayan ganawarsa da Shugaba Buhari
Sakataren Amurka yayi magana kan matsalar tsaro bayan ganawarsa da Shugaba Buhari Hoto: punchng.com
Asali: UGC

"Da farko dai, muna da kyakkyawar alaƙa tsakanin mu, kuma kasarmu a shirye take ta taimakawa Najeriya wajen magance waɗannan matsalolin."

"Amma matakin farko da zamu shigo ciki shine taimakawa Najeriya wajen bada horo, kayan aiki, bada bayanai da kuma abun da yafi muhimmanci kare haƙƙin ɗan adam."

KARANTA ANAN: 75% na ɗaliban jami'ar Jihar Kaduna KASU zasu bar makarantar Saboda ƙarin kuɗi, ASUU

Blinken ya kuma shawarci sauran ƙasashen dake fama da matsalar tsaro da su fara magance tushen abinda ya kawo matsalar a yankin su.

Ya ƙara da cewa:

"Hakanan kuma akwai buƙatar a magance wasu abubuwa da a wani lokaci suke kawo rashin jituwa, rikice-rikice da tsattsauran ra'ayi. Ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan shine ɗaukar hankalin da tafkin Chadi yayi, wanda ya haɗa da ambaliyar da yayi saboda canjin yanayi."

"Wannan ka iya jawo rashin jituwa game da wasu ma'adanai, sabon tsarin tafiye-tafiye da ke saka mutane cikin saɓani, rashin tsaro a ɓangaren abinci, yaɗuwar cututtuka cikin sauƙi. Dukkan waɗannan zasu iya haɗa jama'a wuri ɗaya wanda za'a iya samun yan ta'adda a ciki."

"Ina tunanin wannan yakamata mu fara magancewa, kuma a yadda nasani, shugaba Buhari ya maida hankalinsa a kai sosai"

A wani labarin kuma Kashi 70% na matasan Najeriya yan zaman kashe wando ne, Inji NOA

Hukumar NOA ta bayyana cewa kashi 60% na mutanen Najeriya matasa ne, kuma aƙalla matasan sun kai miliyan N80m.

Hukumar ta kuma bayyana cewa kashi 70% daga cikin matasa miliyan N80 da Najeriya ke dasu basu da cikakkken aikin yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262