Da Ɗumi-Ɗumi: An tsaurara matakan tsaro a zauren majalisa saboda barazanar tsaro

Da Ɗumi-Ɗumi: An tsaurara matakan tsaro a zauren majalisa saboda barazanar tsaro

- Jami'an tsaro sun tsaurara binciken abubuwan hawa a kan hanyar da zata sada ka da zauren majalisar ƙasar nan

- Jami'an dai na ɗaukar dogon lokaci suna bincikar abun hawa, inda ma'aikata da kuma yan jarida ke ɗaukar dogon lokaci kafin su shiga

- A makon nan ne, Gwamnan Neja yace Abuja ma na cikin matsala bayan mayaƙan Boko Haram sun ƙwace iko da wasu yankunan jihar Neja

An tsaurara matakan tsaro a zauren majalisar ƙasar nan saboda jami'an tsaro na ɗaukar dogon lokaci suna bincikar abubuwan hawan dake ƙoƙarin shiga harabar zauren.

KARANTA ANAN: Gwamnatin Bauchi ta dakatar da wani malamin addinin musulunci Daga gudanar da Wa'azi

Binciken abubuwan hawa a yau ya zarta na kowanne rana wanda hakan ya haddasa dogon layi a hanyar shiga zauren majalisar, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

Ma'aikatan wurin da kuma yan jarida suna bata lokaci mai tsawo kafin su sami damar shiga zauren.

Da Ɗumi-Ɗumi: An tsaurara matakan tsaro a zauren majalisa saboda brazanar tsaro
Da Ɗumi-Ɗumi: An tsaurara matakan tsaro a zauren majalisa saboda brazanar tsaro Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Rahotanni sun tabbatar da cewa akwai zargin barazanar tsaro wanda yasa dole aka tsaurara bincike kafin shiga zauren majalisar.

Ƙasar dai na fama da matsalolin tsaro da suka haɗa da; ta'addanci a yankin arewa maso gabas, yan bindiga a yankin arewa maso yamma, rikicin makiyaya a yankin kudu maso yamma da sauransu.

KARANTA ANAN: Sakataren Amurka yayi magana kan matsalar tsaro bayan ganawarsa da Shugaba Buhari

A farkon makonnan ne, gwamnan Neja, Abubakar Bello, yace babban birnin ƙasar nan shima bai tsira ba bayan mayaƙan Boko Haram sun anshe iko da wasu kauyuka a Neja. Jihar Neja dai ta haɗa iyaka da birnin tarayya Abuja.

Hakanan kuma, a ranar Talata, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya nemi taimakon kasar Amurka wajen yaƙi da matsalar tsaro a faɗin ƙasar nan.

A ranar Laraba, majalisar wakilai ta ƙaddamar da kwamitin mutane 40 domin su gano hanyoyin da za'a warware matsalolin tsaron da ƙasar nan ke fama dasu.

A wani labarin kuma Kashi 70% na matasan Najeriya yan zaman kashe wando ne, Inji NOA

Hukumar NOA ta bayyana cewa kashi 60% na mutanen Najeriya matasa ne, kuma aƙalla matasan sun kai miliyan N80m.

Hukumar ta kuma bayyana cewa kashi 70% daga cikin matasa miliyan N80 da Najeriya ke dasu basu da cikakkken aikin yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel