Muna Jin Tsoro, Boko Haram Na Iya Mamaye Abuja – Sanatocin Najeriya Sun Koka

Muna Jin Tsoro, Boko Haram Na Iya Mamaye Abuja – Sanatocin Najeriya Sun Koka

- Bayyanar cewa kungiyar Boko Haram na kara kusantowa kusa da Abuja ya sa wasu jiga-jigan 'yan majalisar dattijan kasar shiga halin fargaba

- Sanatocin da suka firgita sun yi kira ga shugaban kasa da ya gaggauta daukar matakan ceto babban birnin tarayyar kasar nan daga fadawa hannun masu tayar da kayar baya

- Tuni, wata tawaga daga majalisar dattijai ke shirin ganawa da shugaban kasar domin bayyana bukatunsu a fili

Sanatocin Najeriya a ranar Talata, 27 ga Afrilu sun bayyana tsoron cewa mayakan Boko Haram na iya mamaye babban birnin kasar, Abuja.

Sanatocin sun bayyana damuwar su a yayin zaman majalisar bayan wani kudiri, wanda sanata Musa Sani daga jihar Neja ya gabatar.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-duminsa: Buhari ya gana da Zulum kan rashin tsaro

Muna Jin Tsoro, Boko Haram Na Iya Mamaye Abuja – Sanatocin Najeriya Sun Koka
Muna Jin Tsoro, Boko Haram Na Iya Mamaye Abuja – Sanatocin Najeriya Sun Koka Hoto: @NGRSenate
Asali: Twitter

Sani, sanatan da ke wakiltar yankin Neja ta Gabas, ya sanar da takwarorinsa cewa tafiyar awa biyu ne kadai ke tsakanin yan ta’addan da Abuja.

Kalaminsa:

"An watsar da mazaunan wadannan sassan jihar da ke fama da yaki kuma an barsu daga su sai halinsu wanda hakan ya tilasta masu zama cikin mummunan bakin ciki."

Ya kara da cewa garuruwa 42 da ke fadin kananan hukumomin biyu na Shiroro da Munya sun fada karkashin ikon Boko Haram zuwa yanzu inda mazauna kauyuka kusan 5,000 suka rasa matsugunansu a cikin kwanaki uku da suka gabata.

Da yake bayar da gudummawarsa ga kudirin, tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ike Ekweremadu, a cikin nasa jawabin ya ce gwamnatin da Buhari ke jagoranta ta rasa cancantar ta na jagoranci.

Kalaminsa:

“Duk gwamnatin da ba za ta iya kare rayukan mutane ba to ta rasa cancantar ta. Muna buƙatar yin wani abu game da wannan kuma cikin sauri. Idan akwai bukatar mu rufe jihar Neja ko majalisar dattawa domin neman mafita, toh mu yi hakan.”

A matsayin hanyar magance matsalar, majalisar dattijai ta yanke shawarar tura shugabanninta don ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari.

Shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan, ya bayyana cewa zai jagoranci sauran manyan shugabannin majalisar dokokin, domin ganawa da shugaban kasa.

KU KARANTA KUMA: Wani Sanata Daga Jihar Neja Ya bayyana Wani Adadi Mai Yawa Na Ƙauyukan dake Ƙarƙashin Boko Haram

Hakanan majalisar ta yanke shawarar kiran sabbin hafsoshin da aka nada domin yi musu bayani kan matakan da aka dauka na kawo karshen lamarin. Sai dai ba a sanar da ranar yin hakan ba.

A gefe guda, ‘Yan majalisar wakilan tarayya sun yi zama inda su ka tattauna a game da matsalar tsaro da ake fama da ita a garuruwa da-dama na kasar nan a halin yanzu.

Jaridar Vanguard ta fitar da rahoto dazu cewa majalisar tarayyar ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sa dokar ta-baci a kan sha’anin tsaro.

Majalisar wakilan ta na ganin cewa hakan ne zai sa a iya kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng