Da dumi-duminsa: Buhari ya gana da Zulum kan rashin tsaro

Da dumi-duminsa: Buhari ya gana da Zulum kan rashin tsaro

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari saka labule da Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno

- Sun gana ne a daren ranar Litinin, 26 ga watan Afrilu a fadar shugaban kasa da ke Abuja

- Ganawar nasu na zuwa ne bayan hare-haren mayakan Boko Haram a jihar wanda yayi sanadiyar rasa ran sojoji da dama

Shugaba Muhammadu Buhari a daren Litinin ya gana da Gwamnan Borno Babagana Zulum, a Fadar Shugaban Kasa, Abuja.

Ko da yake ana ci gaba da jiran cikakken bayani game da ganawar, amma majiyoyi sun ce tattaunawar ta shafi yanayin tsaro ne a Jihar ta Borno, jaridar The Nation ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Waiwaye: Yadda El-Rufai Ya Nemi Jonathan Ya Tattauna Kan Sakin 'Yan Matan Chibok

Da dumi-duminsa: Buhari ya gana da Zulum kan rashin tsaro
Da dumi-duminsa: Buhari ya gana da Zulum kan rashin tsaro Hoto: The Sun
Asali: UGC

Ayyukan 'yan ta'adda, ciki har da Boko Haram da Islamic State, West African Province (ISWAP), sun tsananta a yankin arewa maso gabashin kasar yan kwanakin nan.

A ranar Lahadin da ta gabata, rahotanni sun ce sojoji sama da 30 ne suka rasa ransu a sanadiyyar harin da ‘yan ta’adda suka kai a kan wani sansanin soji da ke garin Mainok kimanin kilomita 60 daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

A wani labarin, Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya mika ta'aziyyarsa da jajensa ga iyalan sojojin da suka rasu a cikin kwanakin karshen mako yayin yaki da 'yan ta'addan Boko Haram a garin Mainok dake kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

KU KARANTA KUMA: Gbajabiamila Yayi Magana Game da Matsalar Tsaron Najeriya, Ya Bayyana Abin da Buhari Ke Fama da Shi

Zulum a wata takarda da ya fitar ta hannun kakakinsa, Malam Isa Gusau, ya kwatanta sojojin da suka rasa rayukansu a matsayin sadaukai wadanda suka mutu yayin kare Borno da kuma karfin ikon kasar nan.

A cikin ranakun karshen mako ne 'yan ta'adda suka dira garin Mainok mai kusanci da babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel