Wani Sanata Daga Jihar Neja Ya bayyana Wani Adadi Mai Yawa Na Ƙauyukan dake Ƙarƙashin Boko Haram

Wani Sanata Daga Jihar Neja Ya bayyana Wani Adadi Mai Yawa Na Ƙauyukan dake Ƙarƙashin Boko Haram

- Wani sanata daga jihar Neja, ya bayyana cewa kauyuka da dama sun koma ƙarƙashin ikon yan ta'addan Boko Haram a jihar

- Sanatan dake wakiltar mazaɓar jihar Neja ta gabas, Sanata Mohammed Sani Musa, ya faɗi haka ne yayin da yake gabatar da kudiri a gaban majalisa kan kashe-kashen dake faruwa a Neja

- Musa ya ƙara da cewa matuƙar ba'a ɗauki matakin da ya dace ba, to yan ta'addan zasu cigaba da kai hare-haren su ne yadda suka ga dama

Sanatan dake wakiltar mazaɓar Neja ta gabas a majalisar dattijai, Sanata Mohammed Sani Musa, yace kimanin ƙauyuka 42 ne ke ƙarƙashin ikon mayaƙan Boko Haram a jihar Neja.

Wannan na zuwa ne bayan gwamnan jihar Neja, Sani Bello, ya bayyana cewa yan ta'addan sun fara kafa tutocinsu a wasu ƙauyukan jihar, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Cikakken Bayani: Yadda jirgin yaƙin NAF, Boko Haram Suka hallaka sojoji 33 a Mainok

Lokacin da yake magana a gaban takwarorinsa yan majalisar yau Talata, yayin da yake gabatar da kudiri a kan kashe-kashen da ake a ƙananan hukumomin Shiroro, Munya da kuma Rafi, jihar Neja.

Sanator Musa yace sama da mutane 475 aka kashe a yankin da yake wakilta daga watan Janairu 2020 zuwa yanzun.

Ɗan majalisar ya nuna matuƙar damuwarsa cewa tsawon shekaru bakwai kenan yankin Neja ta gabas ke fama da mugayen hare-hare daga yan ta'addan Boko Haram.

Ya ce an samu yawaitar hare-haren ne saboda rashin kulawa da hukumomin tsaro suke baiwa yankin.

Wani Sanata Daga Jihar Neja Ya bayyana Wani Adadi Mai Yawa Na Ƙauyukan dake Ƙarƙashin Boko Haram
Wani Sanata Daga Jihar Neja Ya bayyana Wani Adadi Mai Yawa Na Ƙauyukan dake Ƙarƙashin Boko Haram Hoto: @mohdsanimusa
Asali: Twitter

A jawabin nasa, sanata Musa yace:

"Sun sace mutane da dama, sun kwace musu matan su sannan suka tilasta wa matan zama da mambobin ƙungiyar Boko Haram ɗin. Sun tayar da sansanin sojoji uku a Allawa, Bassa da Zagzaga. Sannan kuma sun kashe wasu daga cikin jami'an tsaro."

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Ahmad Lawan ya rantsar da sabon Sanata a majalisar Dattijai

"Ina mai tabbatar muku da cewa Boko Haram sun kwace kauyuka da dama kuma sun kafa tutocinsu, kamar Kaure, Alawa da Magami."

"Daga watan Maris zuwa yau, mayaƙan Boko Haram sun kashe jami'an tsaro 24 a yankin, sannan kuma sun kashe mutane 16, da yawa kuma suka bar gidajensu domin tseratar da rayuwarsu."

Yace idan wannan matsalar ta cigaba da faruwa, waɗannan yan ta'addan zasu ƙara matsawa wasu ƙauyukan ne, waɗanda basu da wata sana'a Sai Noma.

Kuma a cewarsa hakan zai jawo wa Najeriya ƙarancin abinci da kuma karyewar tattalin arziƙi a ɓangaren Noma.

A wani labarin kuma Dalilin da Yasa Yan Arewa Zasu Fi Son Bola Tinubu Ya Zama Magajin Buhari

Daraktan ƙungiyar magoya bayan Bola Tinubu, Aminu Sulaiman ya bayyana dalilin da yasa yan arewa zasu fi son Tinubu ya gaji shugaba Buhari a zaɓe mai zuwa.

Ya ce jagoran APC ɗin yayi sadaukarwa mai yawa a baya kuma yana da duk wani abu da ake buƙata na jagorancin wannan ƙasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: