Labari mai zafi: ‘Yan Majalisa za su aikawa NSA, Hafsoshin sojoji, shugannin tsaro sammaci

Labari mai zafi: ‘Yan Majalisa za su aikawa NSA, Hafsoshin sojoji, shugannin tsaro sammaci

- Majalisar Tarayya ta bukaci a sa dokar ta-baci kan harkar tsaro a Najeriya

- ‘Yan Majalisar sun nemi duka manyan jami’an tsaro su bayyana a gabansu

- Femi Gbajabiamila ya bayyana matsayar Yan Majalisa a karshen zaman yau

‘Yan majalisar wakilan tarayya sun yi zama inda su ka tattauna a game da matsalar tsaro da ake fama da ita a garuruwa da-dama na kasar nan a halin yanzu.

Jaridar Vanguard ta fitar da rahoto dazu cewa majalisar tarayyar ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sa dokar ta-baci a kan sha’anin tsaro.

Majalisar wakilan ta na ganin cewa hakan ne zai sa a iya kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya.

KU KARANTA: An cafke mutane 240 da ake zargi da satar mutane da fyade

Haka zalika a zaman da aka yi a ranar Talata, 27 ga watan Afrilu, 2021, ‘yan majalisar sun yarda a gayyaci manyan shugabannin tsaro su bayyana a gabansu.

Rahoton ya ce ‘yan majalisar su na son ganin mai ba shugaban kasa shawara akan abin da ya shafi harkar tsaro, Manjo Janar Babagana Mongunu (mai ritaya).

Har ila yau, an bukaci duka hafsoshin sojoji na kasa da shugabannin hukumomin tsaro su bayyana a zauren majalisar domin su yi bayanin halin da ake ciki.

Hafsoshin sojojin da ake sa ran za su hallara a zauren majalisa su ne; Janar Lucky Irabor, Laftana-Janar I. Attahiru, Admiral A.Z Gambo, da Air Marshal I.O Amao.

Labari mai zafi: ‘Yan Majalisa sun aikawa NSA, Hafsoshin sojoji da shugannin tsaro gayyata
Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila
Asali: Twitter

KU KARANTA: Boko Haram sun karbe matan mutane a jihar Neja

Shugaban majalisar wakilai, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya karanto matsayar da majalisar kasar ta cin ma a wannan zaman da su ka yi na farko a makon nan.

Femi Gbajabiamila ya bayyana wannan matsaya ne bayan ‘yan majalisar sun yi sa’o’i hudu su na tattaunawa.

A cewar shugaban majalisar, an dauki wannan mataki na gayyatar manyan jami’an tsaro ne domin a kare jinane da dukiyoyin ‘yan Najeriya da ake ta kashe wa.

Kafin yanzu kun ji cewa daga jiya zuwa yau, an kai hare-hare da su ka yi sanadiyyar mutuwar Bayin Allah da jami'an tsaro rututu da kuma asarar dukiya masu yawa.

Miyagu sun shiga jihohin Borno, Anambra, da Kaduna. Sannan kuma an ji 'yan ta'addan Boko Haram sun fara karfi a Neja, har ta kai sun kafa tutar cin gari da yaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel