Jirgin Yaƙin NAF Ya Jefawa Motar Sojojin Ƙasa Bam Bisa Kuskure

Jirgin Yaƙin NAF Ya Jefawa Motar Sojojin Ƙasa Bam Bisa Kuskure

- Jiragen yakin sojojin saman Nigeria, NAF, ya sakewa sojojin kasan Nigeria bam bisa kuskure a Mainok

- Bam din da jirgin yakin ya saki ya yi sanadin rasuwar sojoji da dama tare da jikkata wasu

- Wani babban soja ya ce an turo motar da aka sake wa bam din ne domin ta kawo wa sojoji dauki kafin aka sake mata bam bisa kuskure

Sojoji da dama sun mutu bayan wani jirgin yaki na rundunar sojojin saman Nigeria ya saki bam kan dakarun sojojin kasa na Nigeria da ke Mainok a jihar Borno, Daily Trust ta ruwaito.

Majiyoyi daban-daban sun bayyana cewa sojoji 30 ne suka riga mu gidan gaskiya a Mainok.

Wasu sojojin sun rasu ne sakamakon bam din da sojojin saman suka saki bisa kuskure yayin da wasu kuma yan ta'adda ne suka halaka su.

DUBA WANNAN: Da duminsa: Ƴan bindiga sun afka jami'a sun sace ɗalibai a Makurɗi

Jiragen Yaƙin NAF Sun Jefa Wa Sojojin Ƙasa Bam Bisa Kuskure
Jiragen Yaƙin NAF Sun Jefa Wa Sojojin Ƙasa Bam Bisa Kuskure. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Majiya daga rundunar sojoji sun shaidawa majiyar Legit.ng cikin sirri cewa wasu kayayyakin sojoji sun bace ciki har da mota mai bindiga sakamakon artabun.

Tuni dai bidiyon harin ya bazu a shafukan intanet.

Da aka tuntube shi a ranar Litinin, Kakakin rundunar sojojin sama, Edward Gabkwet ya ce shima ya ga bidiyon amma ba zai iya tabbatar da ingancinsa ba, yana mai cewa akwai bukatar yin bincike kwakwara.

KU KARANTA: Da Ɗuminsa: Ƴan IPOB Sun Yi Wa Makiyaya Fulani 19 Yankan Rago a Anambra

"Da farko, sun mun tabbatar da ingancin bidiyon.

"Ba zamu rikice ba kawai domin mun ga wani bidiyo a dandalin sada zumunta yana yawo. Sai mun tabbatar da ingancinsa.

"Idan sahihi ne, zai mu yi bincike kan me yasa ya faru da yadda ya faru.

"Haka ake aikin. Ba zai yi wu ba kawai bayan na saurara in iye cewa sahihi ne ko akasin haka ba tare da an bi ka'idojin bincike ba," in ji Gabkwet.

Wani babban soja da baya son a fadi sunansa ya ce motar da aka sakarwa bam din ta kawo sojoji ne domin taimakawa sojojin da ke artabu da yan ta'adda a Mainok.

A wani rahoton daban, Mallam Garba Shehu ya caccaki wadanda suke sukar Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Dr Isa Pantami saboda rashin yafe masa abin da ya yi a baya, Channels Television ta ruwaito.

Ya na ganin rashin yafewa ministan kan maganganun da ya yi na goyon bayan kungiyoyi masu tsatsauran ra'ayi ya fi muni kan laifin da ministan ya aikata.

Babban mai taimakawa shugaban kasar a bangaren watsa labarai ya yi wannan kalaman ne a lokacin da ya bayyana a shirin Politics Today na Channels Television a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel