Da Ɗuminsa: Ƴan IPOB Sun Yi Wa Makiyaya Fulani 19 Yankan Rago a Anambra

Da Ɗuminsa: Ƴan IPOB Sun Yi Wa Makiyaya Fulani 19 Yankan Rago a Anambra

- Wasu da ake kyautata zaton yan kungiyar IPOB ne sun halaka fulani 19 yan gida daya a Anambra

- Rahotanni sun ce maharan sun afka misu ne a daren ranar Asabar inda suka fito da su waje suka dauresu suka yi musu yankan rago

- Wani mazaunin garin da abin ya faru wanda ya nemi a boye sunansa ya ce maharan sun datse wasu sassan jikin mamatan sun tafi da su bayan halaka shanu da dama

Wasu da ake zargi ƴan kungiyar masu neman kafa kasar Biafra, IPOB, sun yi wa makiyaya fulani 19 yankan rago a Igbariam da ke ƙaramar hukumar Oyi ta jihar Anambra.

Rahotanni sun ce ƴan daban sun afka wani bene da makiyaya fulanin ke zama ne misalin ƙarfe 2 na daren ranar Asabar.

DUBA WANNAN: Da duminsa: Ƴan bindiga sun afka jami'a sun sace ɗalibai a Makurɗi

Da Ɗuminsa: Ƴan IPOB Sun Yi Wa Makiyaya Fulani 19 Yankan Rago a Anambra
Da Ɗuminsa: Ƴan IPOB Sun Yi Wa Makiyaya Fulani 19 Yankan Rago a Anambra
Asali: Original

Ɓata garin sun halaka mata 12, maza bakwai da ƙananan yara da ba a san addinsu ba.

An gano cewa bata garin sun fito da wadanda abin ya faru waje, suka cire musu tufafi suka ɗauresu sannan suka yanka su.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa wakilinta ya samu hotuna marasa kyawun gani na gawarwakin wadanda abin ya faru da su.

KU KARANTA: El-Rufai Ya Lissafa Abubuwa 3 da Za a Yi Don Hana Ƴan Bindiga Satar Ɗalibai a Kaduna

Wani mazaunin garin da ya nemi a boye sunansa ya ce bata garin sun datse kan maza uku, suka yanke al'ura da wasu sassan jikin matan suka tafi da su.

Majiyar ta ƙara da cewa bata garin sun kashe shanu 25, sun raunata 19 sannan suka yanka wasu guda biyar.

"Yara biyu suna asibiti a halin yanzu. Ɓata garin sun yi wa wani yaro ɗan wata tara rauni a goshinsa.

"Abin bakin cikin shine dukkan wadanda abin ya faru da su ƴan uwa ne," in ji majiyar.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Anambra, Ikenga Tochikwu bai amsa kira da aka yi masa ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

A wani rahoton daban, Mallam Garba Shehu ya caccaki wadanda suke sukar Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Dr Isa Pantami saboda rashin yafe masa abin da ya yi a baya, Channels Television ta ruwaito.

Ya na ganin rashin yafewa ministan kan maganganun da ya yi na goyon bayan kungiyoyi masu tsatsauran ra'ayi ya fi muni kan laifin da ministan ya aikata.

Babban mai taimakawa shugaban kasar a bangaren watsa labarai ya yi wannan kalaman ne a lokacin da ya bayyana a shirin Politics Today na Channels Television a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164