Da Duminsa: Ƴan Bindiga Sun Afka Jami’a Sun Sace Ɗalibai a Makurɗi

Da Duminsa: Ƴan Bindiga Sun Afka Jami’a Sun Sace Ɗalibai a Makurɗi

- 'Yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace dalibai daga jami'ar Tarayya ta Koyon Aikin Noma da ke Makurdi, FUAM

- Direktan Watsa Labarai da Hulda da Jama'a na jami'ar, Mrs Rosemary Waku ta tabbatar da afkuwar hakan cikin sanarwar da ta fitar a ranar Litinin

- Mrs Rosemary ta ce sun sanar da rundunar 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro da abin ya shafa

'Yan bindiga sun sace wasu daga cikin daliban Jami'ar Koyon Aikin Noma da ke Makurdi, FUAM, a jihar Benue, Daily Trust ta ruwaito.

Mahukunta makarantar sun tabbatar da afkuwar lamarin inda suka ce yan bindigan sun sace dalibai da ba a san adadinsu ba a daren ranar Lahadi.

DUBA WANNAN: El-Rufai Ya Lissafa Abubuwa 3 da Za a Yi Don Hana Ƴan Bindiga Satar Ɗalibai a Kaduna

Da duminsa: Ƴan bindiga sun afka jami'a sun sace ɗalibai a Makurdi
Da duminsa: Ƴan bindiga sun afka jami'a sun sace ɗalibai a Makurdi
Asali: Original

Direktan Watsa Labarai da Hulda da Jama'a na jami'ar, Mrs Rosemary Waku ce ta bada wannan sanarwar a ranar Litinin.

"Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace dalibai da ba a tabbatar da adadinsu ba daga dakunan kwanan daliban FUAM a ranar Lahadi 25 ga watan Afrilun 2021.

"Jami'ar ta sanarwa rundunar yan sanda da sauran hukumomin tsaro da abin ya shafa afkuwar lamarin.

"Kawo yanzu, jami'ar bata ji komai ba daga daliban ko wadanda suka sace su tun afkuwar lamarin," in ji ta.

KU KARANTA: Lalong da Onaiyekan Sun Ziyarci Cibiyar Musulunci Yayin Azumi Don Bada Gudunmawa

Wannan na zuwa ne kasa da mako daya bayan wasu yan bindigan sun sace dalibai daga dakunan kwanansu a Jami'ar Green Field da ke Kaduna.

Kasa da awanni 72 bayan sace su, an tsinci gawarwakin uku cikin daliban da aka sace, biyu mata da namiji daya.

A wani labarin daban, kun ji cewa an naɗa kakakin majalisar wakilan tarayyar Nigeria, Femi Gbajabiamila da Sanatoci uku da ke wakiltar Legas a matsayin mambobin Kwamitin bawa gwamna shawarwari wato GAC.

Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, reshen jihar Legas ne ta bada sanarwar a ranar Laraba, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Sanatoci ukun sune maiɗakin jagorar jam'iyyar APC na ƙasa, Oluremi Tinubu, Solomon Adeola da Tokunbo Abiru.

Asali: Legit.ng

Online view pixel