Waɗanda Suka Ƙi Yafewa Pantami Ne Ke da Matsala, Garba Shehu

Waɗanda Suka Ƙi Yafewa Pantami Ne Ke da Matsala, Garba Shehu

- Kakakin shugaban kasa Garba Shehu ya ce wadanda ba su son su yafe wa Pantami suna da matsala

- Shehu ya ce kowane mutum yana da ikon ya sauya halayensa idan ya gano ya yi kuskure a baya

- Ya yi wannan kalaman ne a matsayin martani ga wadanda suka dage sai Pantami ya yi murabus duk da ya nemi afuwa ya kuma ce ya sauya tunaninsa

Mallam Garba Shehu ya caccaki wadanda suke sukar Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Dr Isa Pantami saboda rashin yafe masa abin da ya yi a baya, Channels Television ta ruwaito.

Ya na ganin rashin yafewa ministan kan maganganun da ya yi na goyon bayan kungiyoyi masu tsatsauran ra'ayi ya fi muni kan laifin da ministan ya aikata.

Waɗanda Suka Ƙi Yafewa Pantami Ne Ke da Matsala, Garba Shehu
Waɗanda Suka Ƙi Yafewa Pantami Ne Ke da Matsala, Garba Shehu. Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Allah Ya Yi Wa Yayan Sarkin Musulmi Rasuwa

Babban mai taimakawa shugaban kasar a bangaren watsa labarai ya yi wannan kalaman ne a lokacin da ya bayyana a shirin Politics Today na Channels Television a ranar Juma'a.

Ya ce, "Ina fada maka mutanen da ke ciga da sukarsa duk da cewa mutumin ya ce ya yi wa kansa laifi, ya yi wa mutane laifi, kuma ya nemi afuwa ya sauya tunaninsa, amma ba su son su yafe masa; sune matsalar ba shi ba."

Kungiyoyi da mutane da dama sunyi ta sukar Pantami saboda kalaman da ya furta a baya na goyon bayan kungiyoyi masu tsatsauran ra'ayi.

KU KARANTA: El-Rufai Ya Lissafa Abubuwa 3 da Za a Yi Don Hana Ƴan Bindiga Satar Ɗalibai a Kaduna

Amma fadar shugaban kasa ta fito ta ce tana tare da Pantami da dukkan yan Nigeria domin ganin anyi musu adalci da kare hakokinsu da suka danganci sadarwa na zamani

Garba ya ce ba dai-dai bane a hana mutum damar ya sauya wasu halayensa idan ya gano akwai kuskure a ciki.

A wani labarin daban, kun ji cewa an naɗa kakakin majalisar wakilan tarayyar Nigeria, Femi Gbajabiamila da Sanatoci uku da ke wakiltar Legas a matsayin mambobin Kwamitin bawa gwamna shawarwari wato GAC.

Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, reshen jihar Legas ne ta bada sanarwar a ranar Laraba, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Sanatoci ukun sune maiɗakin jagorar jam'iyyar APC na ƙasa, Oluremi Tinubu, Solomon Adeola da Tokunbo Abiru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164