Gwamnatin Buhari Za Ta Ci Gaba da Bai Wa Talakawa Tallafin N50,000 Na Korona

Gwamnatin Buhari Za Ta Ci Gaba da Bai Wa Talakawa Tallafin N50,000 Na Korona

- Gwamnatin Buhari ta bayyana cewa, za ta ci gaba da tallafawa 'yan Najeriya da kudaden Korona

- Gwamnatin tuni dama ta fara bada tallafin a karkashin shirin Survival Fund da ta kirkira

- Hakazalika, za ta ci gaba da shirin rajistar kamfani ga kananan 'yan kasuwa don karfafa musu

Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da biyan kudaden tallafi ga gama garin mutane da ‘yan kasuwa a matsayin wani bangare na kokarin ta na rage mummunar tasirin kwayar cutar Korona a kan ‘yan Najeriya, in ji kakakin fadar gwamnati a ranar Lahadi.

Ana biyan kudaden ne a karkashin shirin gwamnatin na Survival Fund, wani bangare na shirin bunkasa tattalin arziki (ESP), gidan talabijin na Channels ta ruwaito.

Kunshin kudi tiriliyan N2.3 na ESP, shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya amince da shi a ranar 24 ga Yuni, 2020.

Kanana da matsakaitan masana'antu (MSME) suna da damar samun tallafin N50,000 a matsayin wani bangare na shirin.

KU KARANTA: 'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Kone Ofishin 'Yan Sanda na Mainok ta Jihar Borno

Gwamnatin Buhari za ta ci gaba da ba Talakawa tallafin N50,000 na Korona
Gwamnatin Buhari za ta ci gaba da ba Talakawa tallafin N50,000 na Korona Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Don raya ayyukan yi, tsarin biyan yana nufin tallafawa kamfanoni 500,000 tare da biyan N50,000 ga kowane ma'aikaci na tsawon watanni uku.

Hakanan ana tallafawa masu sana'ar hannu da masu kasuwancin safara da tallafi na N30,000 na lokaci daya.

A cewar wata sanarwa daga kakakin fadar gwamnati, Laolu Akande, tuni ‘yan Najeriya 319,755 suka ci gajiyar shirin na biyan albashi, yayin da 'yan Nijeriya 265,425 suka ci gajiyar a karkashin shirin masu sana'ar hannu da masu kasuwancin safara.

Tsarin yana kuma taimaka wa kananan 'yan kasuwa domin yin rijista tare da Hukumar Kula da Harkokin Kasuwanci (CAC).

Kimanin kamfanoni 172,129 suka ci gajiyar tallafin rijistar kawo yanzu. Manufar ita ce a yi rajistar sabbin kamfanoni 250,000.

An kiyasta shirin tallafin na Korona zai kubutar da ayyuka miliyan 1.3 a fadin kasar kuma ya shafi mutane 35,000 a kowace jiha, a cewar gwamnati.

An fara cike neman tallafin tun ranar 9 ga watan Fabrairu an kuma rufe a ranar 1 ga watan Maris duk a 2021.

KU KARANTA: APC Ta Fusata da Hare-Hare a Imo, Ta Ce Ba Za Ta Bari Imo Ta Zama Filin Kashe-Kashe Ba

A wani labarin, Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo a ranar Lahadi ya ce "akwai alkawarin Allah" ga Najeriya kuma kasar za ta zama "gidan zaman lafiya, tsaro da ci gaba irin wanda ba a taba ganin irinsa ba a wannan nahiya da ma ta gaba da ita."

Ya yi wannan bayanin ne lokacin da yake jawabi a wajen babban taron shekara-shekara karo na 108 na Babban Taron Baptist na Najeriya a Jihar Ogun, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Farfesa Osinbajo ya kara da cewa Najeriya "za ta kasance cibiyar ci gaban tattalin arziki da kimiyya na karni na 21," a cewar wata sanarwa da mai magana da yawunsa Laolu Akande ya sanya hannu akai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel