'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Kone Ofishin 'Yan Sanda na Mainok ta Jihar Borno

'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Kone Ofishin 'Yan Sanda na Mainok ta Jihar Borno

- 'Yan Boko Haram sun sake kai hari jihar Borno, in da suka kona ofishin 'yan sanda a Mainok

- Mazauna yankin sun bayyana cewa, da yawansu sun tsere zuwa daji don tsira da rayukansu

- Mazaunan sun kuma bayyana cewa, sojojin saman Najeriya sun kawo dauki inda suka fatattaki 'yan ta'addan

Wasu da ake zargin 'yan ta'addan Boko Haram ne sun kona ofishin 'yan sanda na Mainok a ranar Lahadi sakamakon mamayar da maharan suka yi wa sansanin sojoji kafin sojojin Najeriya su fatattake su.

Da yake tabbatar da hakan ga jaridar Leadership, Hakimin Kauyen Mainok, Lawan Tuja Mainok, ya ce ‘yan ta’addan sun mamaye sansanin sojoji da motocin bindigogi shida da misalin karfe 1 na rana kuma suka yi wa sojojin barna.

Hakimin kauyen ya kara da cewa a daidai lokacin da ‘yan ta’addan suka shigo da motocinsu na bindiga, suna harbin iska, wanda hakan ya tilasta mazauna tserewa zuwa gidajensu, yayin da wasu suka gudu zuwa dajin da ke kewaye.

KU KARANTA: Yariman Saudiyya ya Magantu da Mahamat Idriss Deby kan Rasuwar Mahaifinsa

'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Kone Ofishin 'Yan Sanda na Mainok ta Jihar Borno
'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Kone Ofishin 'Yan Sanda na Mainok ta Jihar Borno Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Ya ce bayan kimanin sa’a guda suna harbe-harbe, da isowar jirgin yakin sojojin saman Najeriya, ‘yan ta’addan sun tsere daga yankin don haka harbe-harben ya tsaya.

”‘Yan ta’addan sun zo ne da misalin karfe 1 na rana tare da motocin bindigogi kimanin shida a gaban idanun mu suka shiga cikin sansanin sojoji.

"Sojojin da ke wajen sun yi artabu da ‘yan ta’addan kuma karar harbe-harbe ya tursasa mu zuwa gidajennmu, yayin da wasu suka gudu zuwa cikin dajin da ke kusa da su don tsira.

KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun yi Awon Gaba da Mutane 35, Sun Sace Shanu da Dama a Jihar Neja

A wani labarin, Gwamnan jihar Yobe kuma shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC, a ranar Lahadi ya gana da shugaban hafsoshin tsaro Janar Leo Irabo don tattauna batun harin Boko Haram a Geidam.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Darakta Janar na harkokin yada labarai ga Gwamnan, Mamman Mohammed ya sanya wa hannu a ranar Lahadi.

Mohammed ya ce, tun daga ranar Juma'a ne Buni ya kasance yana tattaunawa da jami'an tsaro don samar da mafita mai dorewa game da kai hare-hare a kan Geidam da al'ummomin kan iyaka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel