Tsohon Sufetan Yan Sanda Ya Bayyana Hanyar da Gwamnati Zata Bi Ta Magance Matsalar Tsaro

Tsohon Sufetan Yan Sanda Ya Bayyana Hanyar da Gwamnati Zata Bi Ta Magance Matsalar Tsaro

- Wani tssohon sufetan yan sandan ƙasar nan ya baiwa gwamnatin tarayya shawarar yadda zata yi ta daƙile matsalar tsaron ƙasar nan da jami'an yan sanda kawai

- Ya ce babu isassun yan sanda a ƙasar nan idan ka kwatanta da yawan jama'ar da Najeriya ke dasu

- A cewar tsohon Sufetan idan har gwamnati ta ɗauki sabbin jami'an yan sanda, sannan kuma ta kula da walwalarsu yadda yakamata to zasu iya magance matsalar tsaro gaba ɗaya

Tsohon sufetan yan sandan ƙasar nan, Ibrahim Kpotun Idris, yayi kira ga gwamnatin tarayya ta ɗauki sabbin jami'an yan sanda matuƙar tana son ta kawo ƙarshen ƙalubalen tsaron da yaƙi ci yaƙi cinyewa.

KARANTA ANAN: Shugaban BUA ya gwangwaje wata jami'a da kyautar kuɗi Biliyan N1bn

Idris yace dalilin da yasa matsalar tsaro take cigaba da ruruwa a ƙasar nan shine saboda rashin isassun jami'an yan sanda da kuma rashin kula da su yadda yakamata.

Tsohon sufetan wanda ya bayyana haka yayin da yake jawabi ga manema labarai a Abuja, yace idan ka kwatanta adadin yan sanda da yawan al'ummar Najeriya, zaka tabbatar da babu isassun jami'an yan sanda.

Tsohon Sufetan Yan Sanda Ya Bayyana Hanyar da Gwamnati Zata Bi Ta Magance Matsalar Tsaro
Tsohon Sufetan Yan Sanda Ya Bayyana Hanyar da Gwamnati Zata Bi Ta Magance Matsalar Tsaro

Idris yace:

"Babbar matsalar itace babu isassun yan sanda, jami'an na aiki ne a wahalce idan ka haɗa da yawan al'ummar da muke dashi a Najeriya.

"Na wani ɗan lokaci, inda gwamnati zata ƙara yawan yan sanda domin daƙile matsalar tsaro, to hakan zai taimaka sosai."

KARANTA ANAN: Gwamnonin Arewa sun bayyana matakin da zasu ɗauka kan kisan ɗaliban jami'ar Greenfield

"Haka kuma, yakamata gwamnati ta gyara buƙatun yan sanda, ta ɓangaren walwala da jin daɗinsu da sauran bukatunsu. Matuƙar gwamnati tayi haka to tabbas ƙasar nan zata dawo yadda aka santa."

"Akwai abubuwa da yawa da yakamata ayi domin ƙara ma jami'an yan sanda ƙarfi, su kuma su sami damar daƙile duk wasu laifuffuka a ƙasar nan." a cewarsa.

Idris ya nuna rashin amincewar sa da shirin ƙirƙiro sabbin jami'an yan sandan jihohi, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Yace ƙirkirar waɗansu jami'ai daban kuma bayan waɗanda ake dasu zai sa tsaro ya ƙara taɓarɓarewa ne kawai.

"Maganar jami'an tsaron yankuna, bana tunanin shine hanya mafita, ina ganin sai-dai su rage ma jami'an yan sandan mu karfin gwuiwa, ina ganin ya kamata gwamnati ta dakatar da wannan shirin cikin gaggawa." inji shi.

A wani labarin kuma Masallacin An-Noor dake Abuja Ya Tara Biliyan N1.3bn Domin Yin Wani Muhimmin Aiki

Cibiyar inganta addinin musulunci (ICICE) ta bayyana cewa an samu 1.3 biliyan daga cikin 3.15 biliyan da ake nema don kara fadada masallacin An-Noor.

Shugaban cibiyar Dr. Kabir Kabo, shine ya bayyana haka ranar Asabar a Abuja , kuma yace za'a fara aikin bada jimawa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel