Shugaban BUA ya gwangwaje wata jami'a da kyautar kuɗi Biliyan N1bn
- Shugaban kamfanin BUA, Abdul-Samad Rabi'u ya bada kyautar kuɗi Biliyan N1bn ga jami'ar Ibadan (UI) domin gudanar da gyara a ɓangarori daban-daban na jami'ar
- Gidauniyar shugaban na ware maƙudan kuɗaɗe a duk shekara domin tallafawa jama'a ta ɓangaren lafiya, ilimi da kuma cigaba
- Daraktan dake kula da alaƙar Kamfanin da gwamnati, wanda shine ya wakilci shugaban, yace wannan gidauniyar na ware dala miliyan $100m domin tallafawa jama'an Najeriya da kuma Africa
Shugaban BUA, Alhaji Abdul-samad Rabi'u ya bada kyautar zunzurutun kuɗi biliyan N1bn ga jami'ar Ibadan (UI) domin gyaran makarantar kamar yadda The Nation ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Gwamnonin Arewa sun bayyana matakin da zasu ɗauka kan kisan ɗaliban jami'ar Greenfield
Alhaji Rabi'u ya bada kyautar ne a wata ziyara da yakai ofishin muƙaddashin shugaban makarantar, Prof. Adebola Babatunde Ekanola, ranar Alhamis.
Alhaji Rabiu, wanda daraktan alaƙar gwamnati a kamfanin BUA, Dr. Aliyu Idi Hong, ya wakilta yace an baiwa jami'ar wannan kyautar kuɗinne saboda yadda take gudanar da ayyukanta masu kyau.
Dr. Hong yace:
"Shugaban BUA, Abdul-Samad Rabiu ya ƙirƙiri gidauniya ta musamman da aka sama suna 'Gidauniyar ASR', an ƙirƙire ta ne domin taimakawa jama'a."
"Bayan yayi aiki tuƙuru a matsayin ɗan Kasuwa, Abdul-samad ya fara tunanin taimakawa jama'a, inda yakeson inganta rayuwar yan Najeriya da kuma yan Africa."
KARANTA ANAN: Zaɓen 2023: Yakubu Dogara ya bayyana halin da Najeriya zata shiga idan Buhari ya sauka a 2023
"A wannan gidauniyar, ana ware maƙudan kuɗaɗe duk shekara da suka kai dala miliyan $100m wajen taimaka wa jama'an Najeriya da kuma Africa. An kasa kuɗin gida biyu, rabinsu an ware don tallafawa a Najeriya, rabin kuma an ware wa Africa."
A jawabin da yayi lokacin amsar tallafin, muƙaddashin shugaban jami'ar ya godewa gidauniyar Abdul-Samad Rabiu (ASR) da gaba ɗaya tawagar Kamfanin BUA bisa wannan huɓɓasa da suka yi.
Prof. Ekanola ya ƙara da cewa hukumar makarantar zata yi amfani da wannan tallafin wajen bada horo ga ɗalibanta domin su zama waɗanda za'a yi alfahari da a duniya.
A wani labarin kuma Haɗa Miliyan N800m Ba Abune Mai Sauƙi Ba, Iyayen Ɗaliban Greenfield Sun Koka
Ɗaya daga cikin iyayen ta bayyana cewa ɗanta ya koma makaranta ranar Talata, amma sai labarin sace shi taji ranar Laraba.
A wani taro da suka yi a Kaduna, iyayen sunce ba zasu iya haɗa waɗannan maƙudan kuɗaɗen da yan bindiga suka nema ba.
Asali: Legit.ng