Masallacin An-Noor dake Abuja Ya Tara Biliyan N1.3bn Domin Yin Wani Muhimmin Aiki

Masallacin An-Noor dake Abuja Ya Tara Biliyan N1.3bn Domin Yin Wani Muhimmin Aiki

- Cibiyar inganta addinin musulunci (ICICE) ta bayyana cewa an samu 1.3 biliyan daga cikin 3.15 biliyan da ake nema don kara fadada masallacin An-Noor

- Shugaban cibiyar Dr. Kabir Kabo, shine ya bayyana haka ranar Asabar a Abuja, kuma yace za'a fara aikin bada jimawa ba

- Ministan Sadarwa da tattalin arziƙin zamani, Isa Pantami ya jawo hankalin mutane kan bada sadaƙa musamman ga mabuƙata

Masallacin An-Noor, Abuja, ya tara kuɗi kimanin 1.3 Biliyan daga cikin 3.15 biliyan da ake buƙata domin faɗaɗa masallacin zuwa mai cin mutane 10,000.

Dr. Kabir Kabo, daraktan cibiyar musulunci ta ƙasa-da-ƙasa (ICICE), shine ya bayyana haka Ranar Asabar kamar yadda PM News ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Shugaba Buhari ne Babban Maƙiyin Haɗin kan Najeriya, inji shugaban ƙungiyar Yarbawa

ICICE itace ke kula da gudanarwar masallacin, an samar da cibiyar ne domin inganta ilimin addinin musulunci, al'adu, goyon bayan al'umma da kuma wanzar da zaman lafiya.

Kabo ya gode ma ɗai-ɗaikun mutane da ƙungiyoyi waɗanda suka bada gudummuwan su don ganin an ƙara ma masallacin girma.

Kabo yace:

"Yau, ina matuƙar farin ciki a matsayina na daraktan wannan cibiya, mun miƙa wannan nasara ga Allah wanda ya bamu damar buɗe wannan gidauniya kuma mutane suka bada gudummuwar su har 1.3 biliyan."

"Muna fatan zamu sami aƙalla 3.0 miliyan, mafi ƙarancin kuɗin da muke buƙata domin gudanar da aikin."

Idan ka duba gaba ɗaya harabar masallacin da irin hada hadar da akeyi, zakaga cewa wurin ya wuce a kirasa masallaci kaɗai, sai-dai ace Cibiyar Musulunci."

Pantami Yayi Magana, Yayin da Masallacin An-Noor Ya Tara Biliyam N1.2bn Domin Yin Wani Muhimmin Aiki
Pantami Yayi Magana, Yayin da Masallacin An-Noor Ya Tara Biliyam N1.2bn Domin Yin Wani Muhimmin Aiki Hoto: destimap.com
Asali: Twitter

"Muna buƙatar ƙara faɗaɗa masallacin daga girman sa na yanzun da yake ɗaukar mutane 1,000 zuwa ɗaukar mutane 10,000, shiyasa muka ƙaddamar da wannan asusun, mun baiwa ɗan kwagilar da zai aikin watanni 24 ya gama." Injishi

KSRANTA ANAN: Yan Sanda sun damƙe mutane huɗu da zargin kashe wani Sabon ango kwana ƙaɗan kafin bikinsa

Sarkin musulmi kuma shugaban majalisar ƙoli ta addinin musulunci, Muhammad Sa'ad Abubakar, ya roƙi mutane da su bayar da gudummuwarsu iya ƙarfinsu domin ganin an ƙarama masallacin girma.

Yace wannan wata dama ce da mutane suka samu domin bada sadaƙa ta hanyar Allah kuma su samu kyakkyawan sakamako saboda aikin su.

Anasa ɓangaren, Ministan Sadarwa da tattalin arziƙin zamani, Sheikh Isa Pantami, ya ƙara jaddada buƙatar mutane masu hali dake rayuwa a yankin, su taimaki marasa ƙarfi.

"Ina ƙara tunatar damu, akwai buƙatar mu taimaki yan uwanmu da dukiyar da Allah ya bamu ta hanyar bada sadaƙa, saboda Allah ya jawo hankalin mu akan mu rinƙa taimakon marasa ƙarfi." inji Pantami

A wani labarin kuma Shugaba Buhari ya yi Allah-wadai da kisan daliban jami'ar Greenfield 3 a Kaduna

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da kisan daliban jami'ar Greenfield da aka sace kwanaki 3 da suka gabata a makarantarsu dake jihar Kaduna.

Buhari ya bayyana cewa wannan hare-hare da kashe-kashen da ake yi a jihar Kaduna abin takaici ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags:
Online view pixel