Gwamnonin Arewa sun bayyana matakin da zasu ɗauka kan kisan ɗaliban jami'ar Greenfield

Gwamnonin Arewa sun bayyana matakin da zasu ɗauka kan kisan ɗaliban jami'ar Greenfield

- Ƙungiyar gwamnonin arewa sun nuna rashin jin daɗinsu da kisan ɗalibai uku daga cikin ɗaliban jami'ar Greenfield da yan bindiga suka sace ranar Talata

- Shugaban ƙungiyar kuma gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong, shine ya bayyana haka a wani saƙo da ya fitar ta bakin daraktan yaɗa labaransa ranar Asabar

- A ranar Jumu'a data gabata ne, jami'an tsaro suka gano gawarwakin ɗalibai uku daga cikin waɗanda aka sace a jami'ar a wani ƙauye dake kusa da makarantar

Ƙungiyar gwamnonin arewa tayi Allah wadai da kisan ɗaliban jami'ar Greenfield da Yan biɓdiga suka yi.

KARANTA ANAN: Shugaba Buhari ne Babban Maƙiyin Haɗin kan Najeriya, inji shugaban ƙungiyar Yarbawa

Shugaban gwamnonin kuma gwamnan jihar Plaateau, Simon Lalong, ya bayyana lamarin da tsantsar jahilci da mugunta, yace ba zasu bar lamarin ya tafi hakanan ba.

Lalaong ya faɗi haka ne a wani jawabi da daraktan yaɗa labaransa, Dr. Makut Macham, ya fitar ranar Asabar a Jos, babban birnin jihar Plateau.

Shugaban gwamnonin yace babu wani uzuri da za'a yi ma kisan ɗalibi wanda ba ruwansa, kawai yana karatu ne domin ya bauta ma ƙasa nan gaba.

Ya kuma ƙara da cewa ƙungiyarsu zata cigaba da haɗa kai da gwamnatin tarayya wajen gano hanyoyin da za'a magance matsalar satar mutane da sauran ayyukan ta'addanci musamman a makarantun yankin arewa.

Gwamnonin Arewa sun bayyana matakin da zasu ɗauka kan kisan da akai ma ɗaliban jami'ar Greenfield
Gwamnonin Arewa sun bayyana matakin da zasu ɗauka kan kisan da akai ma ɗaliban jami'ar Greenfield Hoto: @PLSgov
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Yan Sanda sun damƙe mutane huɗu da zargin kashe wani Sabon ango kwana ƙaɗan kafin bikinsa

A ranar jumu'a aka gano gawar ɗalibai uku daga cikin ɗaliban jami'ar Greenfield da aka sace, a wani ƙauye wanda yake kusa da makarantar.

Yan bindigan sun sace ɗaliɓai a makarantar jami'ar Greenfield dake ƙauyen Kasarmi, kan hanyar Kaduna zuwa Abuja ƙaramar hukumar Chukun ranar Talata.

A wani labarin kuma Masallacin An-Noor dake Abuja Ya Tara Biliyan N1.3bn Domin Yin Wani Muhimmin Aiki

Cibiyar inganta addinin musulunci (ICICE) ta bayyana cewa an samu 1.3 biliyan daga cikin 3.15 biliyan da ake nema don kara fadada masallacin An-Noor.

Shugaban cibiyar Dr. Kabir Kabo, shine ya bayyana haka ranar Asabar a Abuja , kuma yace za'a fara aikin bada jimawa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel