Da duminsa: An harbe manoma guda tara har lahira a jihar Nasarawa

Da duminsa: An harbe manoma guda tara har lahira a jihar Nasarawa

- Mahara sun kashe wasu manoma tara a yankin Ajimaka, wani matsugunin Tiv da ke karamar Hukumar Doma a Jihar Nasarawa

- Mummunan al'amarin ya afku ne a ranar Asabar, 24 ga watan Afrilu

- Sai dai kuma da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na ’yan sanda, ASP Rahman Nansel, ya ce har yanzu rundunar ba ta samu rahoton ba

Wani rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa an kashe wasu manoma tara a yankin Ajimaka, wani matsugunin Tiv da ke karamar Hukumar Doma a Jihar Nasarawa.

Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Asabar, 24 ga watan Afrilu.

Wadanda aka kashe a Doma sune Tsekaa Chiatyo, Kwaghdoo Tsekaa, Sewiesi Tsekaa Bobo Chiatyo, Aondosee Fidelis Aboy, Igba Aduku, da Iwuesi Aseer.

KU KARANTA KUMA: Kashe-kashen Kaduna: Gumi ya bayyana mafita guda 1 ga fashi da makami, ya aike da sako mai muhimmanci ga FG

Da duminsa: An harbe manoma guda tara har lahira a jihar Nasarawa
Da duminsa: An harbe manoma guda tara har lahira a jihar Nasarawa Hoto: @PremiumTimesng
Asali: UGC

An tattaro cewa yan bindigan sun afkawa mutanen ne da misalin karfe biyu na safiyar Asabar, suna harbi ba kakkautawa a iska tare da rera wakokin yaƙi.

Shugaban kungiyar Tiv Development Association (TIDA) a jihar Nasarawa, Kwamared Peter Ahemba, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici.

Ya yi nadamar cewa hare-haren da ake kaiwa mutanen Tiv na jihar, musamman wadanda ke zaune a yankunan kan iyaka tsakanin jihohin Benuwai da Nasarawa, sun zama abin da ake sake samu duk da kokarin da gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule da takwaransa na Benuwai, Dr. Samuel Ortom suka yi don tabbatar da dorewar zaman lafiya.

Ya ce: "A duk lokacin da makiyaya ke da lamuran da suka shafi aiwatar da dokar hana kiwo a fili da gwamnatin jihar Benuwai, sai su zo su far wa mutanenmu (Tiv) a jihar Nasarawa."

“Mu‘ yan asalin Tiv ne na jihar Nasarawa. Mu mutane ne masu son zaman lafiya kuma dole ne makiyaya su daina afkawa mutanenmu kan abubuwan da ba su san komai a kansu ba,” inji shi.

Sai dai kuma, ya bayyana cewa mummunan lamarin ya haifar da raba dubban manoma 'yan kabilar Tibi da muhallinsu a yankin.

Lokacin da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na ’yan sanda, ASP Rahman Nansel, ya ce har yanzu rundunar ba ta samu rahoton ba.

KU KARANTA KUMA: Jami'ar Greenfield: Daga karshe sunaye da hotunan ɗaliban da aka kashe sun bayyana

Ya ce: "Har yanzu rundunar ba ta samu rahoto ba amma da zaran na samu cikakken bayani daga jami'anmu a Doma zan dawo gare ku."

A wani labarin, mun ji cewa akalla yan matan gidan suna 20 yan bindiga suka sace a garin Gidan Bido, dake karamar hukumar Dandume, a jihar Katsina.

A cewar Katsina Post, wannan hari ya auku ne ranar Juma'a misalin karfe daya.

Hakazalika yan bindigan sun yi awon gaba da mutum biyar a garin Unguwar Bawa, duk a karamar hukumar Dandume ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel