Kashe-kashen Kaduna: Gumi ya bayyana mafita guda 1 ga fashi da makami, ya aike da sako mai muhimmanci ga FG

Kashe-kashen Kaduna: Gumi ya bayyana mafita guda 1 ga fashi da makami, ya aike da sako mai muhimmanci ga FG

- Sheikh Gumi ya nuna damuwa game da kisan wasu daliban jami'ar Greenfield da masu garkuwa suka yi

- Gumi ya koka kan cewa gwamnati ta ki tattaunawa da ‘yan fashin

- Malamin, ya roki gwamnatin tarayya da ta bi shawarar sa game da 'yan fashin

Malamin addinin Islama kuma mai shiga tsakani a yakin da ake yi na kawo karshen matsalar 'yan ta'adda a Najeriya, Sheikh Ahmad Gumi, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta yi amfani da shawarwarinsa tare da yin afuwa ga' yan ta'addan da za su ajiye makamansu.

Jaridar The Punch ta bada rahoton cewa Gumi yana mayar da martani ne game da kisan wasu daliban jami'ar Greenfield, Kaduna da wasu yan bindiga suka sace su daga makarantarsu.

Legit.ng ta tattaro cewa Gumi ya fadawa jaridar a ranar Juma’a, 23 ga Afrilu, cewa lamarin ya jaddada matsayinsa cewa yan fashi yanzu suna yaki ne da kasar.

Kashe-kashen Kaduna: Gumi ya bayyana mafita guda 1 ga fashi da makami, ya aike da sako mai muhimmanci ga FG
Kashe-kashen Kaduna: Gumi ya bayyana mafita guda 1 ga fashi da makami, ya aike da sako mai muhimmanci ga FG Hoto: @elrufai
Asali: Facebook

KU KARANTA KUMA: Da dumi-duminsa: Fargaba yayin da 'yan bindiga suka kona kauyen wani gwamna, sun kashe jami'an tsaronsa

Malamin ya ce ba shi da katabus game da lamarin jihar Kaduna saboda gwamnatin jihar ba ta nuna kowani shiri na tattauna da 'yan bindigar ba.

Gumi, wanda ya fito daga jihar Kaduna, ya ce hanya daya tilo da zai sa baki kamar yadda ya yi a jihohin Neja da Katsina ita ce El-Rufai ya sake shawara game da tattaunawa da 'yan fashi.

Ya ce:

"Lamarin ya fara munana kuma ina bukatar goyon bayan gwamnati kafin na iya yin komai, kuma ina ganin akwai babban rashin fahimta da karancin karanta halin da ake ciki a kasa. Don haka, bani da katabus; Ban san ainihin abin da zan iya yi ba a yanzu.”

Gumi ya bayyana kisan daliban Greenfield a matsayin mai halakarwa, abin takaici kuma wanda bai dace ba, yana zargin cewa yakin kabilanci na gudana a kasar.

Malamin ya ce:

“Maganar gaskiya, abin takaici ne matuka. Akwai yakin kabilanci dake gudana, kuma na sha fadarsa. Yaƙi ne amma idan ba ma son yarda da cewa yaƙi ne, za mu ci gaba da shan wahala."

A gefe guda, mun ji cewa an bayyana sunayen dalibai uku na Jami'ar Greenfield da ke Kaduna wadanda 'yan fashi suka kashe a hannunsu.

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: Mahaifiyar sarkin Kano, Maryam Bayero, ta rasu

Jaridar PM News ta ruwaito cewa daya daga cikin daliban da aka kashe shine Abubakar Sadiq Yusuf Sanga, dan Malam Yusuf Mu’azu, darekta a ma’aikatar ayyuka na jihar kuma tsohon shugaban karamar hukumar Jemaa.

An binne Sadik kamar yadda addinin Musulunci ya tanada,a ranar Juma'a, 23 ga Afrilu, daidai da ranar da aka kashe shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng