Jami'ar Greenfield: Daga karshe sunaye da hotunan ɗaliban da aka kashe sun bayyana
- A yanzu an san cewa Jami'ar Greenfield da ke Kaduna ta rasa dalibanta uku da aka sace a ranar Juma’a, 23 ga Afrilu
- Sunayen daliban su ne Abubakar Sadiq Yusuf Sanga, Dorathy Yohanna da Precious Nwakacha
- A cewar gwamnatin jihar, an tsinci gawar daliban ne a wani kauye wanda ba shi da nisa da makarantar
An bayyana sunayen dalibai uku na Jami'ar Greenfield da ke Kaduna wadanda 'yan fashi suka kashe a hannunsu.
Jaridar PM News ta ruwaito cewa daya daga cikin daliban da aka kashe shine Abubakar Sadiq Yusuf Sanga, dan Malam Yusuf Mu’azu, darekta a ma’aikatar ayyuka na jihar kuma tsohon shugaban karamar hukumar Jemaa.
An binne Sadik kamar yadda addinin Musulunci ya tanada,a ranar Juma'a, 23 ga Afrilu, daidai da ranar da aka kashe shi.
KU KARANTA KUMA: Da duminsa: Mahaifiyar sarkin Kano, Maryam Bayero, ta rasu
Sauran mutum biyun da lamarin ya rutsa da su sun hada da Dorathy Yohanna da Precious Nwakacha (‘yan asalin Nnewi da ke cikin jihar Anambra).
Da yake tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Juma'a, kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, ya bayyana cewa an gano gawarwakin wadanda lamarin ya rutsa da su a kauyen Kwanan Bature, wanda ke kusa da jami’ar.
Aruwan ya ce tare da taimakon kwamandan rundunar, Operation Thunder Strike, Laftanar Kanar MH Abdullahi, an kai ragowar daliban dakin ajiye gawa.
KU KARANTA KUMA: Rayuwar kurkuku ta fiye mani, in ji Mallam Gambo wanda ya shafe shekaru 21 a gidan yari
A wani labarin, Gwamnan jihar Kaduna, Nasir el-Rufai, ya bayyana abin da gwamnati za ta yi don dakatar da kai hare-hare a kan makarantu a fadin jihar.
A cewarsa, akwai bukatar gina makarantu kusa da sansanonin soji, jaridar The Cable ta ruwaito.
Ya bayyana hakan ne da yake magana yayin wani shiri a Gidan Talabijin na Najeriya (NTA) a ranar Juma'a, Afrilu 23.
Asali: Legit.ng