Yan bindiga sun yi awon gaba da mata 20 a gidan suna a jihar Katsina

Yan bindiga sun yi awon gaba da mata 20 a gidan suna a jihar Katsina

- Yan bindiga sun kai hari gidan suna, sun debi dimbin mutane

- Kisa da satan mutane ya zama ruwan dare da Arewacin Najeriya

- A kudu kuwa, yan bindiga sun hana jami'an tsaro sakat yayinda suke kai hari ofishohinsu

Akalla yan matan gidan suna 20 yan bindiga suka sace a garin Gidan Bido, dake karamar hukumar Dandume, a jihar Katsina.

A cewar Katsina Post, wannan hari ya auku ne ranar Juma'a misalin karfe daya.

Hakazalika yan binsifan sun yi awon gaba da mutum biyar a garin Unguwar Bawa, duk a karamar hukumar Dandume ranar Asabar.

Dan majalisar dokokin jihar Katsina mai wakiltar mazabar Dandume da garin Unguwar Bawa ne.

Katsina na jihohin Arewacin Najeriya da ke fama a matsalar rashin tsaro.

A ranar 11 ga Disamba, 2020, yan bindiga sun yi awon gaba da daliban makarantar GSSS Kankara 344, kafin aka samu nasarar kubutar da su.

DUBA NAN: Sai kun kara mana kudi zamu iya kawar da yan ta'adda, Shugaban Hafsan Soji Attahiru

Yan bindiga sun yi awon gaba da mata 20 a gidan suna a jihar Katsina
Yan bindiga sun yi awon gaba da mata 20 a gidan suna a jihar Katsina Credit: Desert Herald
Asali: UGC

KU KARANTA: Munanan hare-hare, garkuwa da mutane, da kashe-kashe 6 da suka auku Laraba

A bangare guda, gwamnatin jihar Katsina ta amince da tura karkuna gadin makarantun kwanan jihar domin taimakawa jami'ar tsaro wajen dakile yan bindiga masu garkuwa da mutane.

Kwamishanan ilimin jihar, Dr Badamasi Charanchi, ya bayyana cewa gwamnatin ta yanke shawaran haka ne domin karfafa matakan tsaro a makarantun kwanan jihar, rahoton TheNation.

Yace: "An bamu shawaran tura karkuna kowace makaranta saboda suna da horaswa na gano wani mai yunkurin kutse fiye da dan Adam."

"Wadannan karnukan idan aka tura su, zasu ankarar da dalibai da sauran jami'an tsaro idan wasu yan bindiga na kokarin zuwa."

Asali: Legit.ng

Online view pixel