El-Rufai Ya Lissafa Abubuwa 3 da Za a Yi Don Hana Ƴan Bindiga Satar Ɗalibai a Kaduna

El-Rufai Ya Lissafa Abubuwa 3 da Za a Yi Don Hana Ƴan Bindiga Satar Ɗalibai a Kaduna

- Gwamnan Kaduna Nasiru El-Rufai ya bayyana wasu abubuwa da ya dace ayi domin dakile harin yan bindiga a makarantun jihar

- Gwamnan ya ce ya kamata a samar d sansanin sojoji kusa da makarantu sannan a yi katanga a makarantun musamman na kwana da ke kauyuka

- Har wa yau, gwamnan ya ce akwai bukatar a kara adadin jami'an tsaro da ke jihar domin aikin ya fi karfin wadanda suke jihar a yanzu

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya bada shawarar cewa a rika gina makarantu kusa da sansanin sojoji domin kare harin yan bindiga a jihar, The Cable ta ruwaito.

Yayin da ya ke magana a shirin gidan talabijin na kasa, NTA, a ranar Juma'a, El-Rufai za a iya dakile harin idan sojoji za su iya isa makarantun cikin mintuna 30.

El-Rufai: A Riƙa Gina Makarantu Kusa da Sansanin Sojoji Saboda Ƴan Bindiga
El-Rufai: A Riƙa Gina Makarantu Kusa da Sansanin Sojoji Saboda Ƴan Bindiga. Hoto: @thecableng
Asali: Facebook

A ranar Talata, an sace dalibai daga wata jami'a mai zaman kanta da ke Kaduna, wannan shine hari na uku da ake kaiwa makarantun jihar a wannan shekarar.

DUBA WANNAN: Sunayen sabbin alƙalai 18 da Buhari ya amince da naɗinsu a kotun daukaka ƙara

El-Rufai ya ce jihar na cigaba da aiki kan matakan dakile wasu hare-haren a gaba ciki har da ware kudade don gina katanga a makarantu.

Ya kuma ce Kaduna na bukatar karin sojoji a wuraren da abubuwan ke faruwa domin kallubalen tsaron ya fi karfin yan sanda da jami'an tsaro na Civil Defence wato NSCDC.

Gwamnan ya zayyana matakai uku da jihar za ta dauka don dakile hare-haren na yan bindigan

1. Gina katanga a makarantu domin rashin katanga na saukaka wa bata gari yin kutse

2. Samar da karin jami'an tsaro da suka hada da sojojin, Civil Defence, Masu tsaro na sirri, yan sa-kai da wadanda za su rika sa ido domin su sanar da hukuma idan sun ga an kawo hari.

3. Samar da sansanin sojoji kusa da makarantu ta yadda sojoji za su iya isa makarantun cikin minti 30

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Fursunoni sunyi yunƙurin tserewa daga gidan yari a Kano

El-Rufai ya ce binciken da suka yi ya nuna cewa yan bindigan sun fi kai hari makarantun kwana da ke kauyuka sannan da dare suke kai harin.

A wani labarin daban, kun ji cewa an naɗa kakakin majalisar wakilan tarayyar Nigeria, Femi Gbajabiamila da Sanatoci uku da ke wakiltar Legas a matsayin mambobin Kwamitin bawa gwamna shawarwari wato GAC.

Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, reshen jihar Legas ne ta bada sanarwar a ranar Laraba, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Sanatoci ukun sune maiɗakin jagorar jam'iyyar APC na ƙasa, Oluremi Tinubu, Solomon Adeola da Tokunbo Abiru.

Asali: Legit.ng

Online view pixel