Jam'iyyar APC ta bawa matar Tinubu da Gbajabiamila muƙami mai muhimmanci

Jam'iyyar APC ta bawa matar Tinubu da Gbajabiamila muƙami mai muhimmanci

- Jam'iyyar APC reshen jihar Legas ta naɗa matar Tinubu da Gbajabiamila mambobin kwamitin GAC

- Kwamitin na bawa gwamna shawara itace kwamiti mafi girma a jam'iyyar ta APC a Legas

- Mr Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Babajide Sanwo-Olu suma mambobi ne na kwamitin

An naɗa kakakin majalisar wakilan tarayyar Nigeria, Femi Gbajabiamila da Sanatoci uku da ke wakiltar Legas a matsayin mambobin Kwamitin bawa gwamna shawarwari wato GAC.

Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, reshen jihar Legas ne ta bada sanarwar a ranar Laraba, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Jam'iyyar APC ta bawa matan Tinubu da Gbajabiamila muƙami mai muhimmanci
Jam'iyyar APC ta bawa matan Tinubu da Gbajabiamila muƙami mai muhimmanci. Hoto: @PremiumTimesNG
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kotun shari'a ta raba aure a Zamfara saboda tsabar girman mazakutar miji

Sanatoci ukun sune maiɗakin jagorar jam'iyyar APC na ƙasa, Oluremi Tinubu, Solomon Adeola da Tokunbo Abiru.

A cewar Seye Oladejo, mai magana da yawun jam'iyyar APC reshen jihar Legas, an naɗa su ne saboda gudunmawar da suka kwashe shekaru suna bayarwa domin cigaban tattalin arziki da siyasa a jihar.

"Naɗin da aka masu zai basu wata dama na cigaba da bada jagoranci na gari don habbaƙa demokradiyyar mu.

"Muna musu fatan alheri a dukkan abin da za su yi," a cewar sanarwar.

KU KARANTA: Maigida ta nemi na kwanta da ita a madadin biyan kuɗin haya, in ji Saurayi

Kwamitin bawa gwamna shawarwari ita ce kwamiti mafi ƙarfi a jam'iyyar ta APC reshen jihar Legas.

Mambobin kwamitin sun hada da manyan masu ruwa da tsaki a jam'iyyar da ke jihar da za su rika sa ido kan yadda ake gudanar da harkokin jam'iyya.

Mr Ahmed Bola Ahmed Tinubu da Babajide Sanwo-Olu suma mambobi ne na kwamitin.

A wani labarin daban kun ji cewa 'yan sanda a jihar Kano sun ceto wata yarinya mai shekaru 15, Aisha Jibrin, da iyayenta suka kulle ta a daki tsawon shekaru 10 a Darerewa Quaters a karamar hukumar Fagge ta jihar Kano.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce mahaifiyarta Rabi Muhammad tana hannunsu amma mahaifinta ya tsere.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce mahaifiyarta Rabi Muhammad tana hannunsu amma mahaifinta ya tsere.

Asali: Legit.ng

Online view pixel