Sunayen sabbin alƙalai 18 da Buhari ya amince da naɗinsu a kotun daukaka ƙara
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin sabbin alkalai 18 na kotunan daukaka kara a Nigeria, The Cable ta ruwaito.
Kwamitin Kolin Shari'a ta Kasa, NJC, Karkashin jagorancin Ibrahim Muhammad, Alkalin Alkalan Nigeria, CJN, a watan Maris ya mika sunayensu ga shugaban kasa domin a musu karin girma.
A cikin wasikar da ya aike wa CJN din, Farfesa Ibrahim Gambari, Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, ya ce Buhari ya amince da bukatar yi wa alkalan karin girma.
DUBA WANNAN: Maigida ta nemi na kwanta da ita a madadin biyan kuɗin haya, in ji Saurayi
"Ina farin cikin sanar da kai cewa Mai girma Shugaban kasa ya amince da nadin wadannan a matsayin alkalan kotun daukaka kara saboda matayinsu a kotun kamar yadda ya ke a sashi na 237 da 238 na kundin tsarin mulkin 1999," a cewar wasikar.
Shugaban kasar ya kuma yi wa sabbin alkalan da aka nada fatan alheri a yayin da za su cigaba da ayyukansu a kotunan daukaka kara.
Ga jerin sunayen alkalan:
KU KARANTA: Kotun shari'a ta raba aure a Zamfara saboda tsabar girman mazakutar miji
- Bature Isah Gafai
- Muhammad Ibrahim Sirajo
- Waziri Abdul-Azeez
- Yusuf Alhaji Bashir
- Usman A. Musale
- Jauro Ibrahim Wakili
- Abba Bello Mohammed
- Mohammed Danjuma
- Danlami Zama Senchi
- Mohammed Lawal Abubakar
- Hassan Muslim Sule
- Amadi Kenneth Ikechukwu
- Peter Oyinkenimiemi Affen
- Sybil Onyeji Nwaka Gbagi
- Olasumbo Olanrewaju Goodluck
- Banjoko Adebukunola Adeoti Ibironke
- Olabode Abimbola Adegbehingbe
- Bola Samuel Ademola
A wani labarin daban kun ji cewa 'yan sanda a jihar Kano sun ceto wata yarinya mai shekaru 15, Aisha Jibrin, da iyayenta suka kulle ta a daki tsawon shekaru 10 a Darerewa Quaters a karamar hukumar Fagge ta jihar Kano.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce mahaifiyarta Rabi Muhammad tana hannunsu amma mahaifinta ya tsere.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Kiyawa cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce mahaifiyarta Rabi Muhammad tana hannunsu amma mahaifinta ya tsere.
Asali: Legit.ng