Mako biyu da yin aurenta amarya ta fara korafi, ta ce mijinta yana aikenta barkatai

Mako biyu da yin aurenta amarya ta fara korafi, ta ce mijinta yana aikenta barkatai

- Abena Moet wacce ta yi aure kasa da makonni uku ta ba mutane da yawa mamaki a shafukan sada zumunta da cewar da tayi babu wani abu na musamman game da aure

- A wani bidiyo mai ban dariya, ta ambaci cewa a cikin aure, kawai miji na aiken matar ne yadda ransa yake so

- An gano ta a cikin bidiyo tana kallon kafadunta don tabbatar da cewa mijinta baya sauraron abunda take fadi

Shahararriyar matashiyar nan ta kasar Ghana, Abena Moet, ta haddasa cece kuce game da ra’ayinta a kan aure bayan shafe kusan makonni uku a gidan miji.

A cikin bidiyon barkwancin da ke yawo a shafukan sada zumunta, Abena Moet ta nuna cewa daga abin da ta gani, da zaran kin yi aure a matsayinki na mace, toh kawai mijinki zai ta aikenki ne yadda ransa ke so.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan bindiga sun sake kona wani ofishin yan sanda a kudu maso gabas

Mako biyu da yin aurenta amarya ta fara korafi, ta ce mijinta yana aikenta barkatai
Mako biyu da yin aurenta amarya ta fara korafi, ta ce mijinta yana aikenta barkatai Hoto: Abena.Moet
Asali: UGC

An gano ta a bidiyon tana kallon kafaɗarta don tabbatar da cewa sabon mijin nata ba ya jin abunda take fadi a bidiyon nata.

Kalli bidiyon a kasa:

Abena Moet ta yi aure a wani kasaitaccen biki da ya bazu a yanar gizo a ranar 27 ga waran Maris, 2021.

KU KARANTA KUMA: ‘Kada ku ji tsoron harbin bindiga’, Ministan tsaro ga dakarun sojojin Najeriya

A wani labarin kuma, rundunar yan sanda reshen jihar Enugu ta kama wata mata yar shekara 29, Nnenna Egwuagu, da zargin kashe ɗan kishiyarta dan shekara uku, Wisdom Egwuagu.

Lamarin ya faru ne a garin Umulumgbe dake ƙaramar hukumar Idi, jihar Enugu ranar 9 ga watan Afrilu kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa matar da ake zargin ta baiwa yaron wani abu dake ɗauke da guba, kuma hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel