Yan sanda sun kama wata mata da zargin ta kashe ɗan kishiyarta da guba

Yan sanda sun kama wata mata da zargin ta kashe ɗan kishiyarta da guba

- Rundunar yan sandan jihar Enugu ta kama wata matashiyar mata da zargin kisan ɗan kishiyarta.

- Matar da ake zargin ta amsa laifinta, amma tace ta yi haka saboda mijinta baya bata kulawa sam da ita da yayanta

- Kwamishinan yan sandan jihar ya yi kira ga ma'aurata da su ƙara danƙon soyayya a tsakaninsu don gudun faruwar irin haka nan gaba

Rundunar yan sanda reshen jihar Enugu ta kama wata mata yar shekara 29, Nnenna Egwuagu, da zargin kashe ɗan kishiyarta dan shekara uku, Wisdom Egwuagu.

KARANTA ANAN: Kotu ta yanke ma fitacciyar jarumar shirya fina-finai hukuncin watanni uku a gidan yari saboda hoton tsiraici

Lamarin ya faru ne a garin Umulumgbe dake ƙaramar hukumar Idi, jihar Enugu ranar 9 ga watan Afrilu kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa matar da ake zargin ta baiwa yaron wani abu dake ɗauke da guba, kuma hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar ta Enugu, Daniel Ndukwe, ya ce yan sandan dake yankin sun kama matar ne bayan mijinta, Justine Egwuagu, ya kai musu rahoton abinda yafaru.

Yan sanda sun kama wata mata da zargin ta kashe ɗan kishiyarta da guba
Yan sanda sun kama wata mata da zargin ta kashe ɗan kishiyarta da guba Hoto: @mobilepunch
Asali: Twitter

Ndukwe yace:

"Matar da ake zargin ta amsa laifinta na baiwa yaron wani abu da zai cutar dashi, sai-dai ta ce ta yi haka ne saboda rashin kulawar mijinta akanta da ɗiyarta, shiyasa take son yaron ya kwanta rashin lafiya wataƙila hakan yasa mijin ya kashe kuɗi akanshi wajen nema masa lafiya."

KARANTA ANAN: Ministan Wutar Lantarki ya nemi gafarar yan Najeriya bisa saka su a duhu

"Daga baya an tabbatat da mutuwar yaron a asibiti, daga baya aka kai gawarsa ɗakin ajiye gawarwaki."

"Mun gano mazubin gubar da ta yi amfani dashi wajen kisan yaron, kuma jami'an mu na cigaba da bincike."

Kakakin yan sandan ya ƙara da cewa kwamishinan jihar, Mohammed Aliyu, ya yi Allah wadai da lamarin inda ya shawarci ma'aurata da su ƙara danƙon soyayya a tsakaninsu.

A wani labarin kuma Wasu Yan bindiga sun kashe mutane huɗu a wani sabon hari da suka kai jihar Taraba

Wasu yan bindiga sun sake kai sabbin hare-hare a wasu ƙauyuka guda biyu na jihar Taraba, inda suka kashe mutum huɗu.

Yan bindigar sun kai hari kauyukan ne da daren Laraba, suka kashe mutum huɗu tare da jikkata wasu da dama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262