‘Kada ku ji tsoron harbin bindiga’, Ministan tsaro ga dakarun sojojin Najeriya
- Ministan tsaro a Najeriya ya bukaci rundunar sojoji ta Operation Lafiya Dole da kada su ji tsoron harbin bindiga
- Ya bayyana cewa, ba zasu taba tsallake kaddarar mutuwarsu ba ko da kuwa suna dakin kwanansu ne
- Ya bayyana haka ne a wata ziyarar da ya kai Maiduguri babban birnin jihar Borno a jiya Lahadi
Yayin da Najeriya ke yaki da ‘yan ta’addan Boko Haram a yankin arewa maso gabas, Ministan Tsaro, Magashi Bashir, ya nemi rundunar Operation Lafiya Dole da kada su ji tsoron harbe-harbe daga 'yan ta’addan, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.
Ya ba da wannan umarnin ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin wata ziyara da ya kai wa rundunar a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, tare da shugaban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Lucky Irabor da sauran shugabannin rundunonin tsaro.
KU KARANTA: Jihar Ondo za ta fara gwanjon shanun da ta kama da lalata gonakin 'yan jihar
"Kada ku ji tsoron kowane harsashi, harsashin zai zo kuma zai tafi," in ji shi.
"Idan ba a nufi ku mutu ta hanyar harsashi ba, ba za ku taba mutuwa ba amma idan ta harbin bindiga za ku mutu, ko da a cikin dakin kwanan ku ne harsashi zai zo ya same ku, wanda shi ne abin da na fuskanta a lokacin aikina."
A cewar Ministan, dalilin ziyarar shi ne don duba irin gwagwarmayar da sojojin ke yi na Operation Lafiya Dole da kuma karfafa musu gwiwa.
KU KARANTA: Nasara daga Allah: 'Yan sanda sun sheke 'yan bindiga 6 a jihar Neja
A wani labarin, Ministan tsaro, Bashir Magashi, ya ce nan bada jimawa ba gwamnatin tarayya zata fara ɗaukar sabbin sojoji a faɗin ƙasar nan.
Lokacin da yake jawabi a hedkwatar sojojin dake Maiduguri yayin da ya jagoranci shugaban tsaro CDS, General Lucky Irabor, da sauran shuwagabannin tsaro suka kai ziyara.
Magashi yace shirin na ɗaya daga cikin ƙoƙarin gwamnati na ganin ta kawo ƙarshen ta'addanci kamar yadda Channels TV ta ruwaito.
Asali: Legit.ng