Ana sauran sa'o'i 2 daurin aure, mota ta bige ango, ya sheka lahira a Nasarawa

Ana sauran sa'o'i 2 daurin aure, mota ta bige ango, ya sheka lahira a Nasarawa

  • Wani taron biki ya tashi bayan angon yayi mutuwar farat daya a ranar bikin
  • Daya daga cikin abokan marigayin angon ne ya bada labarin yadda lamarin ya faru
  • Ana sauran sa'o'i kadan daura auren ne mota tayi ciki da ango inda yace ga garinku

Mutuwar wani dan Najeriya kasa da sa'o'i biyu kafin bikin auren shi ya gigita jama'ar yankin Ikyangedu dake jihar Nasarawa.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, mota ce ta bige angon mai suna John Abugu yayin da yaje karbo rigar da zai saka wurin daurin auren daga shagon mai wanki da guga.

Amarya mai suna Rosemary Hudu, 'yar kasuwa ce wacce ta fada tsananin jimami bayan jin labarin mutuwar ango Abugu.

A yayin bayyana damuwarta, Rosemary tace ta so a ce mutuwa tayi tare da angonata.

Kara karanta wannan

Yadda Matar Aure Ta Zama Mai Aikin Goge-goge Don Tura Mijinta Makaranta A Kasar Waje, Bidiyon Ya Yadu

KU KARANTA: NDLEA ta damke 'yan kasar Chadi da Nijar dake samarwa 'yan ta'adda miyagun kwayoyi

Ana sauran sa'o'i 2 daurin aure, mota ta bige ango, ya sheka lahira a Nasarawa
Ana sauran sa'o'i 2 daurin aure, mota ta bige ango, ya sheka lahira a Nasarawa. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

KU KARANTA: Ban sake bacci ba tun bayan da aka kashe sojoji a Benue, Ortom

Ta ce: "Na so a ce nima na mutu ta yadda za a birnemu tare. Har yanzu ban yadda ba cewa mijina ya mutu ana sauran sa'o'i kadan daura aurenmu. Ba zan iya cewa komai ba, amma duk inda yake zan kasance tare dashi."

Wani abokin marigayin ango mai suna Julius, yace yana tare da mamacin lokacin da hatsarin ya faru a ranar Asabar, 10 ga watan Afirilun 2021.

Yayin bada labarin yadda lamarin mai matukar firgitarwa ya faru, ya ce: " Da yaso zuwa wurin mai wanki da guga, na ce zan tuka babur din amma sai yace kada in damu zai tuka.

Kara karanta wannan

Yan Sanda Sun Kama Matashi Dan Shekara 20 Da Ake Zargin Yana Garkuwa Da Mutane, Sun Kwato Kayayyaki

"Yana bani labarin wani abokinsa da zai zo ya kaisu wurin bikin da motar angon kuma ya mayar dasu gida bayan bikin. Saboda farin cikin dake tare da shi, bai kalla ko ina ba kawai ya shiga babbar hanyar inda mota kirar Hilux tayi ciki damu.

"Tuni aka gaggauta mika mu asibiti kuma aka fara bamu taimakon likitoci. Ko a asibitin, tare ake duba mu. Amma bayan mintuna kadan, lamarin shi ya kara kamari inda ya fara zubda jini ta ido, hanci da kunne kuma ya mutu."

A wani labari na daban, tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Jonathan, ya ce Babangida Aliyu, tsohon gwamnan jihar Neja yayi karya da yace gwamnonin PDP na arewacin Najeriya sune suka kayar dashi a 2015 ta hanyar hade masa kai.

A ranar Juma'a, Aliyu yace gwamnonin PDP na jihohin arewacin Najeriya sun soki bukatarsa ta zarcewa bayan ya ki cika alkawarinsa na hakura da mulki a wa'adin farko.

"Tunda hakan ya ci karo da yarjejeniyarmu ta farko a jam'iyyar, kuma mu gwamnonin arewa muke ganin za a cuce mu idan Jonathan yayi nasara, sai muka tashi muka hana hakan faruwa," yace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel