Yan Sanda Sun Kama Matashi Dan Shekara 20 Da Ake Zargin Yana Garkuwa Da Mutane, Sun Kwato Kayayyaki

Yan Sanda Sun Kama Matashi Dan Shekara 20 Da Ake Zargin Yana Garkuwa Da Mutane, Sun Kwato Kayayyaki

  • Jami'an yan sanda a jihar Bauchi sun cafke wani matashi dan shekaru 20 kan zargin garkuwa da mutane
  • An samo damin kudi, bindiga, alburusai da sauransu a hannun matashin wanda yace mallakin ubangidansa ne
  • Kwamishinan yan sandan jihar Bauchi, Umar Sanda, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai

Bauchi - Rundunar yan sandan Bauchi tace ta kama wani matashi dan shekaru 20 wanda ake zaton mai garkuwa da mutane ne a jihar.

Kwamishinan yan sandan Bauchi, Umar Sanda, ne ya sanar da hakan a ranar Talata, 18 ga watan Oktoba a wani taron manema labarai kan ayyukan rundunar, jaridar TheCable ta rahoto.

Jami'an yan sanda
Yan Sanda Sun Kama Matashi Dan Shekara 20 Da Ake Zargin Yana Garkuwa Da Mutane, Sun Kwato Kayayyaki Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Sanda ya ce an kama mai laifin wanda ya fito daga Tashan Daudu Soro da ke karamar hukumar Ganjuwa na jihar a watan Saumba kan zargin kasancewarsa da hannu a fashi da makami, garkuwa da mutane da mallaka makamai.

Kara karanta wannan

‘Yan Sanda Sun Bindige Masu Garkuwa da Mutane 2, Sun Samo Kudin Fansa N8.4m a Bauchi

Ya bayyana cewa kayayyakin da aka samo daga hannun wanda ake zargin sun hada da kudi N8,466,000, bindigar toka da alburusai 92, wayoyin hannu takwas, MP3 daya, babur daya, adda da sauransu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sai dai kuma, wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa kayayyakin mallakin ubangidansa ne.

A cewar yan sandar, wanda ake zargin yace ubangidansa ya fita da shi ne kan babur dinsa domin aiki a matsayin mai kiwo lokacin da aka kama shi, amma ubangidan nasa ya tsere.

Ya kuma ce a ranar 7 ga watan Satumba da misalin karfe 4:00 na rana wata tawaga da ke fatrol a hedkwatar yan sanda da ke Maina-Maji a karamar hukumar Alkaleri na jihar, sun kai samame mabuyar miyagu.

A yayin samamen, yan sandan sun kashe wasu mutum biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne.

Kara karanta wannan

An Gurfanar da Mutumin da Ya Shiga Babban Kanti, Ya Sace Bibul 4

Ya ce:

“Da isarsu wajen, masu garkuwa da mutanen sun bude wuta kan jami’an yan sanda kuma yayin da suke mayar da martani, sun kashe biyu daga cikin masu garkuwa da mutanen nan take sannan aka kama daya.”

Kayayyakin da aka kwato yayin samamen sun hada da bindigar AK-47 da alburusai 29.

Sanda ya kara da cewar rundunar yan sanda na ci gaba da jajircewa don ba al’ummar Bauchi kariya.

‘Yan Bindiga Sun Farmaki Wani Gari A Zamfara, Sun Kashe Mutum Daya Da Sace Wasu 8

A wani labarin, mun ji cewa 'Yan bindiga dauke da makami sun farmakin garin Hayin Banki da ke karamar hukumar Anka a jihar Zamfara a daren ranar Litnin inda suka kashe mutum daya da kuma awon gaba da wasu takwas.

Majiyoyi daga hedkwatar karamar hukumar sun sanar da Channels TV cewa yan bindigar sun mamayi yankin ne da misalin karfe 11:30 na dare sannan suka fara harbi kan mai uwa da wahabi.

Kara karanta wannan

"Ita Ta Nemeni Da Soyayya": Dan Jarida Makaho Yayi Tsokaci Kan Aure da rayuwarsa

Mazauna yankin sun ce wasu daga cikin mutanen da aka sace sun kasance ma’aikatan wani kamfanin ruwa da wani manajan gonar kaji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel