Yadda Matar Aure Ta Zama Mai Aikin Goge-goge Don Tura Mijinta Makaranta A Kasar Waje, Bidiyon Ya Yadu

Yadda Matar Aure Ta Zama Mai Aikin Goge-goge Don Tura Mijinta Makaranta A Kasar Waje, Bidiyon Ya Yadu

  • Wani magidanci da ke zaune a kasar waje ya fito fili ya nuna rawar ganin da matarsa ta taka don taimaka masa a Kanada
  • A wani bidiyo da ya yadu a TikTok, mutumin magantu kan yadda sahibar tasa ta zama mai aikin goge-goge don tura shi makaranta
  • Bidiyon ya haddasa cece-kuce inda sauran masu amfani da TikTok suka bayyana ra’ayoyinsu

Wani bidiyon TikTok ya nuno wani magidanci yana kwararo ruwan yabo ga matarsa kan tura shi makaranta da tayi.

Shafin @diandersons ne ya wallafa bidiyon sannan ya hasko mutumin yana cewa matarsa ta zama mai aikin goge-goge don ganin ya samu ingantaccen ilimi.

Miji da mata
Yadda Matar Aure Ta Zama Mai Aikin Goge-goge Don Tura Mijinta Makaranta A Kasar Waje, Bidiyon Ya Yadu Hoto: TikTok/@diandersons.
Asali: UGC

Ya jinjinawa duk matan kirki da suka tallafawa iyalinsu sannan ya sarawa matarsa.

A nata bangaren, matar ta fadama mutumin da ke mata tambayoyi cewa don tsira a rayuwa, dole sai mutum ya ci abinci kuma don cin abinci dole sai mutum ya yi aiki.

Kara karanta wannan

Matashi Ya Garzaya Masallaci Bayan Ya Lashe miliyan N38 A Caca Da Ya Buga Da N800, Bidiyon Ya Yadu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aiki a bangarenta ya hada da zama mai goge-goge don samun madogara idan lokacin haihuwa ya zo.

Bidiyon ya taba zukatan mutane da dama a TikTok yayin da mutane suka yi martani masu dadi. Da dama sun nuna sha’awarsu ga ma’auratan.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@MarvelousMargz ya ce:

"Ina fatan ba za ka taba y da hin watsi da hakan ba?"

@faithlynfarquhars0 ta yi martani:

"Dan Allah kada ka ci mutuncinta wannan matar kirkin."

@user1458961448950 ta yi martani:

"Zan yi aikin goge-goge don tura kaina makaranta ba namiji ba. Mijina na aiki sannan yana makaranta."

Kyakkyawar Budurwa Mai Shekaru 38 Ta Bazama Neman Miji A Intanet,Ta Fashe Da Kuka A Bidiyo

A gefe guda, wata kyakkyawar budurwa yar Najeriya mai suna Princess Mimi ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta koka kan cewa har yanzu bata auru ba duk da yawan shekarunta.

Kara karanta wannan

Har da cire riga: Bidiyon mutumin da ya birkita zaman lafiyan banki saboda an taba kudinsa

Matashiyar mai shekaru 38 ta wallafa wani bidiyo a TikTok inda ta dungi sharban kuka a cikin wata mota yayin da take fallasa asirin zuciyarta.

Princess ta ce zata cika shekaru 39 a bana, kuma har yanzu bata yi aure ko mallakar da nata na kanta ba kuma bata da wani tsayayye da zai fito neman aurenta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel