Jonathan ga Aliyu: Kai babban makaryaci ne, bani da yarjejeniya da gwamnonin PDP na arewa

Jonathan ga Aliyu: Kai babban makaryaci ne, bani da yarjejeniya da gwamnonin PDP na arewa

- Goodluck Jonathan, tsohon shugaban kasan Najeriya ya kira Babangida Aliyu da babban makaryaci akan ikirarinsa

- Jonathan ya bukaci Aliyu da ya kawo takardar shaida ko kuma shaidar mutum a kan yarjejeniyar da yace sun yi

- A cikin makon nan ne Babangida Aliyu yace Jonathan ya karya musu alkawari ne, haka yasa suka ki goya masa bayan zarcewa

Tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Jonathan, ya ce Babangida Aliyu, tsohon gwamnan jihar Neja yayi karya da yace gwamnonin PDP na arewacin Najeriya sune suka kayar dashi a 2015 ta hanyar hade masa kai.

A ranar Juma'a, Aliyu yace gwamnonin PDP na jihohin arewacin Najeriya sun soki bukatarsa ta zarcewa bayan ya ki cika alkawarinsa na hakura da mulki a wa'adin farko.

"Tunda hakan ya ci karo da yarjejeniyarmu ta farko a jam'iyyar, kuma mu gwamnonin arewa muke ganin za a cuce mu idan Jonathan yayi nasara, sai muka tashi muka hana hakan faruwa," yace.

KU KARANTA: NDLEA ta damke 'yan kasar Chadi da Nijar dake samarwa 'yan ta'adda miyagun kwayoyi

Jonathan ga Aliyu: Kai babban makaryaci ne, bani da yarjejeniya da gwamnonin PDP na arewa
Jonathan ga Aliyu: Kai babban makaryaci ne, bani da yarjejeniya da gwamnonin PDP na arewa. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun tsallaka katanga, sun sace basarake

Tuni ikirarin Aliyu ya samu martani daga Jonah Jang, tsohon gwamnan jihar Filato inda ya karyata hakan tare da cewa baya cikin gwamnonin da suka yi wa Jonathan zagon kasa.

A yayin magana a kan ikirarin, Reno Omkri, tsohon hadimin Jonathan, a wata takarda da ya fitar a madadin ubangidansa, yace babu wata yarjejeniya a baki ko a rubuce a tsakanin Jonathan da gwamnonin PDP na arewa na cewa ba zai nemi zarcewa ba.

Kamar yadda takardar tace, Jonathan ya kalubalance tsohon gwamnan Neja da ya bayyana shaidarsa a kan yarjejeniyar.

Tsohon shugaban kasan yace Aliyu ya bada wani ikirari mai sukar hakan bayan da aka tambayesa dalilinsa na kin goyon bayan shi a littafin Segun Adeniyi.

"Babangida Aliyu babban makaryaci ne. Bari in fasa muku ikirarinsa ta yadda zaku gane komai tare da gane karyar," takardar tace.

"Babu wannan yarjejeniya, a rubuce ko a baki. Tunda yace a rubuce aka yi komai, toh Babangida Aliyu ya fito da takardar. Idan kuma ya canza maganarsa yace ba a rubuce take ba, toh ya kawo shaidarsa."

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta damke wani likita tare da wasu mutum 7 a kan zarginsu da ake yi da taimakawa 'yan bindiga a fadin jihar.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Ibrahim Dosara, ya bayyana wannan a jawabin da yayi wa manema labarai a Gusau a ranar Alhamis inda yace an kama likitan a kauyen Kamarawa dake karamar hukumar Isa ta jihar Sokoto.

Kwamishinan yace jami'an rundunar Operation Puff Adder ne suka kama likitan a zarginsa da suke masa na samar da kayan sojoji ga 'yan bindigan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng