Ban sake bacci ba tun bayan da aka kashe sojoji a Benue, Ortom

Ban sake bacci ba tun bayan da aka kashe sojoji a Benue, Ortom

- Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya bayyana cewa bai sake bacci ba tun bayan kisan sojoji 11 a jiharsa

- Gwamnan yace tabbas ya shiga tashin hankali kuma mulkinsa zai kokarta wurin tsamo masu laifin

- Ministan tsaro ya sanar da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari da rundunar sojin Najeriya sun matukar shiga damuwa a kan kisan

Samuel Ortom, gwamnan jihar Benue, ya ce bai sake iya runtsa bacci ba tun bayan da aka kashe sojoji 11 a jiharsa. An kashe sojojin a kauyen Bonta dake karamar hukumar Konshisha a Benue.

Gwamnan a ranar Laraba ya yi wa shugaban kasan ta'aziyya tare da rundunar sojin a kan lamarin da ya faru, The Cable ta ruwaito.

Ya yi wannan jawabin ne yayin da Bashir Magashi, ministan tsaro da kuma hafsoshin tsaro suka kai masa ziyara a Makurdi.

KU KARANTA: Mai rajin kare hakkin dan Adam ta zargi Sowore da karbar tallafi da sunanta babu izininta

Ban sake bacci ba tun bayan da aka kashe sojoji a Benue, Ortom
Ban sake bacci ba tun bayan da aka kashe sojoji a Benue, Ortom. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Mahaifiyar amarya ta tsere da sadakin diyarta, ta bar madaura aure da Lahaula

"Ban yi bacci ba tun bayan kashe sojoji da aka yi," gwamnan yace.

Ortom ya mika godiya ga jami'an tsaro a kan goyon bayansu da gudumawarsu, ballantana sojoji dake tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Gwamnan yace ya umarci masu ruwa da tsaki a Konshisha da su tsamo masu laifin.

Ya dauka alkawarin cewa mulkinsa zai goyi baya tare da hada kai da jami'an tsaro domin tabbatar da cewa an kama masu laifin kuma an hukuntasu.

A bangarensa, ministan tsaro ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari da dakarun sojin Najeriya sun matukar fusata da wannan kisan.

"Rundunar sojin Najeriya tayi matukar bakin cikin kisan da aka yi wa sojoji hadi da wani Kyaftin a karamar hukumar Konshisha ta jihar Benue," yace.

“Wannan lamarin ba zai sa sojojin su sare ba daga aiwatar da ayyukansu na kare rayuka da dukiyoyi a kasar nan.

“Domin karfafa guiwar sojojin, dole a tsamo masu laifin tare da tirsasasu su fuskanci fushin hukuma."

A wani labari na daban, babbar kotun tarayya da ta samu shugabancin Mai shari'a Hadiza Shagari a ranar Laraba, ta yankewa gagararren mai safarar miyagun kwayoyi, Ibrahim Ali, hukuncin shekaru 15 a gidan yari babu tara.

Kafin a kama shi a watan Nuwamban shekarar da ta gabata, Ali ya kasance mai safara tare da siyar da miyagun kwayoyi a garin Katsina.

A wata tattaunawa da manema labarai da hukumar NDLEA reshen jihar Katsina tayi, kwamandan hukumar, Momoudu Sule, ya sanar da manema labari cewa matashin mai safarar miyagun kwayoyin ya shiga hannu kuma an dinga mishi nasiha kada ya koma ruwa amma a banza.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel