Zaɓen 2023: Wani Jigon APC ya bayyana dalilin da zaisa yan siyasa su yaudari Bola Tinubu a 2023

Zaɓen 2023: Wani Jigon APC ya bayyana dalilin da zaisa yan siyasa su yaudari Bola Tinubu a 2023

- Wani mamba kuma jigo a jam'iyya mai mulki ta APC yana jin tsoron muradin Bola Tinubu na tsayawa takarar shugan ƙasa a 2023

- Majiyar ta bayyana dalilin da zaisa jigon APC ɗin y samu koma baya idan ya yanke shawarar tsayawa takara

- sai dai har yanzun jami'iyyar ta APC ba ta yanke shawar wanda zai taka mata takara a zaɓe mai zuwa ba

Wani jigon jam'iyyar APC a ƙaramar hukumar Amuwo-Odofin dake jihar Lagos, ya bayyana cewa akwai yuwuwar yan siyasar arewa su yaudari Tinubu idan ya yanke shawarar fitowa takarar shugaban ƙasa.

KARANTA ANAN: Ministan Sadarwa Isa Pantami ya nesanta kansa da wasu kalmomi da yayi a baya kan Wasu ƙungiyoyin Yan ta'adda

Bola Tinubu na ɗaya daga cikin jigogin da suka ƙirƙiri jam'iyyar APC kuma shi na hannun daman shugabn ƙasa Muhammadu Buhari ne.

Wani mamba a APC, wanda ya zanta da Legit.ng amma ya nemi a sakaya sunanshi, ya gargaɗi Tinubu da ya ɗauki darasi daga abinda yafaru da MKO Abiola.

Ana ganin dai MKO Abiola shine ya lashe zaɓen da aka gudanar a ranar 12 ga watan Yuni.

Mutumin ya shawarci babban jigon APC, Bola Tinubu, da ya cigaba da jan ragamar jam'iyyar maimakon ya dage sai ya fifo neman takarar shugaban ƙasa.

Ya bayyana cewa yana jin tsoron maƙiyan Tinubu zasu bayyana kansu idan ya fito takara kuma hakan zai iya sashi ya faɗi zaɓen.

Zaɓen 2023: Wani Jigon APC ya bayyana dalilin da zaisa yan siyasa su yaudari Bola Tinubu a 2023
Zaɓen 2023: Wani Jigon APC ya bayyana dalilin da zaisa yan siyasa su yaudari Bola Tinubu a 2023 Hoto: @AsiwajuTinubu
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Yan sanda sun kama wata mata da zargin ta kashe ɗan kishiyarta da guba

Mutumin yace:

"Idan kai ba yaron Tinubu bane, to baka da tabbas ɗin za'a tsayar dakai takara a jam'iyyar APC musamman a yankin kudu maso yamma."

"Baba bai kamata yana saka kansa a irin waɗannan al'amuran jam'iyyar ba. Ya daina saka baki akan wa za'a tsaida takara a jihohin kudu maso yamma."

"Idan har Baba bai daina shiga irin waɗannan lamuran ba, to mutane zasu mishi tawaye."

Har yazuwa yanzuɓ dai, Tinubu bai bayyana burinsa na tsayawa takarar shigaban ƙasa a hukumance ba, amma rahotanni a kafafen sada zumunta na ƙara alaƙanta shi da kujerar zaɓen 2023.

A wani labarin kuma Kotu ta yanke ma fitacciyar jarumar shirya fina-finai hukuncin watanni uku a gidan yari saboda hoton tsiraici

Wata Kotu daka zaman ta a Accra, babban birnin ƙasar Ghana ya yanke ma wata jarumar shirin wasan kwaikwayo hukuncin zaman gidan gyaran hali na watanni uku.

An yanke ma jarumar hukuncin ne bayan ta aikata laifin bayyana hoton tsiraici a shafinta na kafar sada zumunta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel