Kotu ta yanke ma fitacciyar jarumar shirya fina-finai hukuncin watanni uku a gidan yari saboda hoton tsiraici

Kotu ta yanke ma fitacciyar jarumar shirya fina-finai hukuncin watanni uku a gidan yari saboda hoton tsiraici

- Wata Kotu daka zaman ta a Accra, babban birnin ƙasar Ghana ya yanke ma wata jarumar shirin wasan kwaikwayo hukuncin zaman gidan gyaran hali na watanni uku

- An yanke ma jarumar hukuncin ne bayan ta aikata laifin bayyana hoton tsiraici a shafinta na kafar sada zumunta

- Jarumar wacce aka fi sani da Akuapem Poloo, ta amsa laifinta bayan ta bayyana a gaban kotu

An yanke wa Fitacciyar jarumar shirya fina-finai a ƙasar Ghana, Rosemond Alade Brown, wacce akafi sani da Akuapem Poloo, hukuncin zaman gidan yari na tsawon watanni uku bisa nuna tsiraici da tayi a wani hoto da ta saka a kafar sada zumunta.

KARANTA ANAN: Ministan Wutar Lantarki ya nemi gafarar yan Najeriya bisa saka su a duhu

A ranar Jumu'a, wata kotu dake zamanta a Accra, babban birnin ƙasar ta bayyana cewa jarumar zata yi zaman gidan yarinta ne a keɓance kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Kotun ta kara da cewa wannan hukuncin zai zama izini ga wasu dake da niyyar aikata makamancin abinda Poloo ta aikata.

Poloo dai ta turo hotunan ne a kafafen sada zumunta a watan Yuni, 2020, don taya ɗanta murnanar cika shekaru bakwai da haihuwa.

Kotu ta yanke ma fitacciyar jarumar shirya fina-finai hukuncin watanni uku a gidan yari saboda hoton tsiraici
Kotu ta yanke ma fitacciyar jarumar shirya fina-finai hukuncin watanni uku a gidan yari saboda hoton tsiraici Hoto: #Akuapem_poloo
Asali: Instagram

Mutane da yawa ba suji daɗin abinda jarumar ta yi ba, yayinda daraktan kare hakkin ƙananan yara na ƙasar ta Gwana, Bright Appiah, ya shigar da ƙara kotu yana roƙon a hukunta ta.

KARANATA ANAN: Shugaban Bankin Sterling Ya ɗora alhakin tsallake Najeriya da Tuwita ta yi Kan yan Najeriya

Akuapem Poloo ta roƙi gafara a kan abinda ta yi, inda ta bayyana cewa ba'a fahince ta bane, ta ɗauki hoton ne don ta nuna ma mutane su rinƙa yab ma mahaifiyarsu.

Sai dai, irin wannan ya saɓa ma dokar yan sandan ƙasar, dalilin hakan yasa aka kama jarumar shirin fim din.

Da farko dai jarumar ta musant zargin da ake mata, amma daga bisani ranar Larabar data gabata ta amince da laifinta a lokacin data bayyana a gaban kotu.

A wani labarin kuma UNICEF ta roƙi yan Najeriya da su koma a sake yi musu allurar rigakafin COVID19 karo na biyu

UNICEF ta roƙi yan Najeriya waɗanda aka yiwa allurar rigakafin korona da su sake komawa a tsira musu allurar a karo na biyu.

A cewar UNICEF ɗin hakan zai ƙara ma ƙwayoyin halittar jikin mutum ƙarfi sosai wajen yaƙar cutar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262