Ministan Sadarwa Isa Pantami ya nesanta kansa da wasu kalmomi da yayi a baya kan Wasu ƙungiyoyin Yan ta'adda

Ministan Sadarwa Isa Pantami ya nesanta kansa da wasu kalmomi da yayi a baya kan Wasu ƙungiyoyin Yan ta'adda

- Ministan Sadarwa da tattalin arziiƙin zamani, Isa Pantami, ya nesanta kansa da wasu maganganu da yayi lokacin yana matashi

- Ministan yace ya canza da yawa daga cikin waɗannan maganganun saboda ƙarin ilmi da kuma gogewa da yayi

- Ya ce a musulunci akwai irin waɗannan domin ko manyan malaman addinin da ake ji da su, irin su Imamu Malik sun yi fatawa kuma suka canza daga baya

Ministan sadarwa da tattalin arziƙim zamani, Dr. Isa Pantami, ya ce ya canza da yawa daga cikin fatawoyinsa da yayi a kan Alƙa'ida da Taliban.

KARANTA ANAN: Yan sanda sun kama wata mata da zargin ta kashe ɗan kishiyarta da guba

A kwanakin nan dai an hurawa ministan wuta kan wasu maganganu da yayi can a baya na goyon bayan masu tsattsauran ra'ayi.

Masu amfani da kafafen sada zumunta na neman shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya Sauke shi daga muƙaminsa idan yaƙi ya ajiye da kansa.

Yayin da yake amsa wata tambaya a wajen karatun fassarar Alƙur'ani mai girma da ya saba yi a watan Ramadan a masallacin An-Noor Abuja, ministan yace yanzun yafi gogewa kuma ya canza da yawa daga cikin matsayarsa a baya.

Yace waɗannn jita-jita da raɗe-raɗin da wasu ke yi akansa duk siyasa ce kuma ba zaka hana ayi maka hassada ba matuƙar kana riƙe da wata amana kuma kana ƙoƙarin sauke wannan amanar yadda yakamata.

Ministan Sadarwa Isa Pantami ya nesanta kansa da wasu kalmomi da yayi a baya kan Wasu ƙungiyoyin Yan ta'adda
Ministan Sadarwa Isa Pantami ya nesanta kansa da wasu kalmomi da yayi a baya kan Wasu ƙungiyoyin Yan ta'adda Hoto: @DrIsaPantami
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Kotu ta yanke ma fitacciyar jarumar shirya fina-finai hukuncin watanni uku a gidan yari saboda hoton tsiraici

A jawabin da yayi lokacin da yake amsa tambayar ranar Asabar a Abuja, Pantami yace:

"Tsawon shekaru 15 nan baya naje jihohi da dama a ƙasar nan harda ƙasar Nijar ina karantar da mutane hatsarin ta'addanci. Naje Katsina, Borno, Kano, Gombe da Difa dake jamhuriyar Nijar nayi wa'azi a kan hatsarin ta'addanci."

"Na haɗu da mutane da yawa waɗanda suka ruɗu da fatawar Boko Haram, kuma na yi ƙoƙarin jawo hankalin matasa da yawa sun bar wannan aƙida sun dawo hanya madaidaiciya."

"Wasu fatawoyin da nayi a baya waɗanda wasu ke ɗakkowa sun magana akai yanzun, nayi su ne bisa fahimtata a wancan lokacin. Na canza da yawa daga cikin irin waɗannan maganganun saboda na samu ilmi kuma naƙara gogewa."

Malamin addinin ya bada misali da manyan malaman addinin musulunci irinsu Imamu Malik, Shafi'i da sauransu, su kansu sunyi fatawa kuma daga baya suka gane kuskure ce kuma suka canza.

"Mafi yawancin maganganun da ake ɗakkowa yanzun na yi su ina yaro lokacin. Na fara nasiha a gaban jama'a tun ina ɗan shekara 12 zuwa 13" inji Pantami.

A wani labarin kuma wani lauya ya bayyana Dalilin da yasa Sheikh Isa Pantami ya yi Muƙabala da Tsohon shugaban Boko Haram

Lauyan ya ce Pantami ya yi muƙabalar ne don ya ƙalubalanci irin koyarwar da Yusuf ɗin ke yi domin ta saɓa da koyarwar addinin musulunci.

Lauyan ya kuma rubuta wasiƙa zuwa ga shugaban Jaridar Daily independent da kuma sufetan yan sandan ƙasar nan kan lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262