Yajin Aikin Likitoci: Zamu gayyaci Ministar Kuɗi tazo ta mana bayani dalla-dalla, Kakakin Majalisa

Yajin Aikin Likitoci: Zamu gayyaci Ministar Kuɗi tazo ta mana bayani dalla-dalla, Kakakin Majalisa

- Kakakin majalisar wakilan ƙasar nan, Femi Gbajabiamila, ya ce majalisarsa zata gayyaci ministar kuɗi, Zainab Ahmed, don tattaunawa kan buƙatun likitoci

- Ya kuma nuna jin daɗin sa bisa janye yajin aiki da ƙungiyar likitocin ta yi saboda shigowar majalisa cikin maganar

- Anasa jawabin shugaban ƙungiyar ta NARD ya nuna jin daɗin sa bisa ziyarar da yan majalisar wakilan suka kawo musu har Hedkwatar su

Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya ce zasu gayyaci ministar kuɗi, Zainab Ahmed, domin tazo ta musu bayani akan wasu buƙatun ƙungiyar Likitocin ƙasar nan NARD.

A ranar Asabar ɗin data gabata ƙungiyar likitoci NARD ta janye yajin aiki da ta fara tun 1 ga watan Afrilu bayan ƙulla yarjejeniya da gwamnatin tarayya.

KARANTA ANAN: Bayani Dalla-Dalla: Rukunin Mutane 3 da suka cancanci su sami bashi daga CBN na Kuɗin COVID19

Likitocin ƙasar nan dai sun shiga yajin aiki ne saboda rashin cika musu alƙawurra da gwamnatin tarayya tayi na kuɗaɗen da suke binta.

A jawabin da yayi lokacin da suka yi taro da NARD ranar Talata, Gbajabiamila, ya ce majalisarsu zata gayyaci ministar kuɗi don su tattauna da ita kan yadda za'a kutsa buƙatun NARD a ƙarin kasafin kuɗi da ake yi.

Yajin Aikin Likitoci: Zamu gayyaci Ministar Kuɗi tazo ta mana bayani Dalla-Dalla- Kakakin Majalisar Wakilai
Yajin Aikin Likitoci: Zamu gayyaci Ministar Kuɗi tazo ta mana bayani Dalla-Dalla- Kakakin Majalisar Wakilai Hoto: @Femigbaja
Asali: Twitter

Kakakin majalisar yace: "Ko kundin tsarin mulki ya yi magana a kan ayyuka masu muhimmanci, amma babu wani aiki da yafi kare lafiya muhimmanci."

"Zamu saka ido don ganin an yi abinda ya dace kan dukkan buƙatun ƙungiyar ku NARD."

"Zamu yi duk abinda zamu iya kuma muke da damar yi, zamu gayyaci ministar kuɗi a mako mai zuwa sabida mu tattauna yaza'a yi mu saka waɗannan buƙatun naku a ƙarin kasafin kuɗi."

Kakakin majalisar ya ƙara cewa sun zaɓi su zo su gana da shuwagabannin Likitocin ne a hedkwatar su don su nuna jin daɗin su kan janye yajin aikin da suka yi.

KARANTA ANAN: Lokaci ya yi da zamu koma ga Allah, Mu baiwa Talakawa saɗaƙa a watan Ramadana, Inji Atiku

"Ziyarar da muka kawo muku na nuni da cewa muna tare da ku saboda muhimmancin likitoci bazai misaltu ba, kuma muna godiya a gareku da kuka janye yajin aiki."

"Mun zo nan ne mu gode muku bisa janye yajin aiki kuma mu ƙara baku tabbacin majalisar mu tare da majalisar zartarwa, zasu yi duk abinda ya kamata ayi."

A jawabinsa, shugaban ƙungiyar likitocin ya nuna jin daɗinsa da yan majalisar wakilan suka kai musu ziyara kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Ya kuma gode ma majalisar kan saurin shiga maganar da ta yi wanda hakan yasa ƙungiyar ta janye yajin aikin.

A wani labarin kuma Dalilin da yasa Sheikh Isa Pantami ya yi Muƙabala da Tsohon shugaban Boko Haram

Ɗaya daga cikin lauyoyin Ministan sadarwa, Sheikh Isa Pantami, ya bayyana dalilin da yasa ministan ya yi muƙabala da tsohon shugaban Boko Haram , Muhammad Yusuf.

Lauyan ya ce Pantami ya yi muƙabalar ne don ya ƙalubalanci irin koyarwar da Yusuf ɗin ke yi domin ta saɓa da koyarwar addinin musulunci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel