Dalilin da yasa Sheikh Isa Pantami ya yi Muƙabala da Tsohon shugaban Boko Haram - Lauya

Dalilin da yasa Sheikh Isa Pantami ya yi Muƙabala da Tsohon shugaban Boko Haram - Lauya

- Ɗaya daga cikin lauyoyin Ministan sadarwa, Sheikh Isa Pantami, ya bayyana dalilin da yasa ministan ya yi muƙabala da tsohon shugaban Boko Haram, Muhammad Yusuf

- Lauyan ya ce Pantami ya yi muƙabalar ne don ya ƙalubalanci irin koyarwar da Yusuf ɗin ke yi domin ta saɓa da koyarwar addinin musulunci

- Lauyan ya kuma rubuta wasiƙa zuwa ga shugaban Jaridar Daily independent da kuma sufetan yan sandan ƙasar nan kan lamarin

Michael Numa, ɗaya daga cikin lauyoyin ministan sadarwa, Sheikh Isa Pantami, ya bayyana dalilin da yasa malamin ya yi muƙabala da tsohon shugaban Boko Haram.

KARANTA ANAN: Wasu Yan Bindiga sun sake kai hari ofishin 'Yan sanda a Cross Rivers

Lauyan ya ce Pantami ya yi muƙabala da Muhammad Yusuf (tsohon shugaban Boko Haram) ne shekaru da yawa da suka gabata domin ya ƙalubalanci koyarwarsa data saɓa ma addinin musulunci.

Hakanan kuma lauyan ya ce ministan bai taɓa shiga cikin jerin sunayen masu ɗaukar nauyin yan ta'adda ba saboda yana da alaƙa da Yusuf.

Numa ya faɗi haka ne a wata doguwar wasiƙa da ya rubuta kuma ya saka ma hannu a ranar 12 ga watan Afrilu, 2021, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Dalilin da yasa Sheikh Isa Pantami ya yi Muƙabala da Tsohon shugaban Boko Haram - Lauya
Dalilin da yasa Sheikh Isa Pantami ya yi Muƙabala da Tsohon shugaban Boko Haram - Lauya Hoto: @DrIsapantami
Asali: Twitter

Ya yi adireshin wasiƙar tasa zuwa Darakta kuma editan jaridar Daily independent. Ya yi ma wasiƙar take da 'Karerayin jawabai da aka yi wa babban mutum, Isa Pantami, ministan sadarwa da tattalin arziƙi'

KARANTA ANAN: Zuwan Ramadana: APC ta raba kayan Abinci cike da Manyan Motocin ɗaukar kaya 130 ga talakawa

Hakanan kuma, lauyan ya yi kwafin wasiƙar zuwa Sufetan yan sanda na ƙasa, da kuma wasu daractocin sashin ayyukan ƙasa, da hukumar fasaha.

Lauyan ya cigaba da cewa rahoton da jaridar Daily independent ta wallafa ya bayyana ƙasar amurka ta saka minista pantami a cikin yan ta'addan da tasa ma ido Saboda zargin yana da alaƙa da tsohon shugaban Boko Haram.

Sai dai mai mabiyin dokar ya bayyana rahoton da "Ƙarya, ƙeta, da kuma shaci faɗi" ya ƙara da cewa an shirya haka ne dan aɓata ma ministan suna.

Sai dai malamin addinin musuluncin, Isa Pantami, kuma ministan sadarwa ya ce ya kasance yana ƙalubalantar dukkan ta'addanci sama da shekaru 15 da suka wuce.

A wani labarin kuma Gwamnan CBN ya bayyana babban dalilin da yasa Shugaba Buhari ke yawan ciyo bashi

Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Dr. Godwin Emefiele ya bayyana babban dalilin da yake tilasta gwamnati ta ciyo bashi

Gwamnan ya ce ciwo bashi ba laifi bane kuma ba zunubi bane, amma akwai wajabcin sanya ido a kan ƙuɗin da aka amso da kuma hanyar da aka yi amfani da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel