Bayani Dalla-Dalla: Rukunin Mutane 3 da suka cancanci su sami bashi daga CBN na Kuɗin COVID19

Bayani Dalla-Dalla: Rukunin Mutane 3 da suka cancanci su sami bashi daga CBN na Kuɗin COVID19

- Gwamnatin Najeriya ta ƙirƙiro da hanyoyi da dama domin rage raɗaɗin da annobar COVID19 ta jefa ɗai-ɗaikun yan Najeriya da kuma yan kasuwa

- Ɗaya daga cikin abun da ta ƙirƙiro shine shirin bada rance daga CBN wanda akaima laƙabi da TCF kuma bankin NIRSAL MICROFINACE ke tafiyar da shi

- Zamu yi bayani dalla-dalla a kan irin mutanen da suka cancanta su nemi rancen na TCF daga bankin Microfinance.

Kamar yadda muka sani gwamnatin tarayya ta ƙirƙiro da sabbin tsare-tsare don rage raɗaɗin da annobar COVID19 ta jefa yan Najeriya a ciki.

Sai-dai duk da haka wasu daga cikin yan Najeriya na cikin duhu kan ko sun cancanta su shiga ɗaya daga cikin tsare-tsaren ko basu cancanta ba.

KARANTA ANAN: A Karon farko, Gwamnan Nasarawa ya rantsar da mace a matsayin babbar Mai Shari'a ta jihar

Zamu maida hankali ne akan shirin da babban bankin ƙasa CBN ya fito dashi na TCF, kuma zamu bayyana rukunin yan najeriyan da suka cancanta su shiga tsarin bada rancen.

Kamar yadda aka bayyana a kwanakin baya, CBN ya ƙirkiro shirin TCF ne a matsayin wani ƙunshi da zai taimaka wajen rage raɗaɗin da annobar korona ta haifar wa yan Najeriya.

Bayani Dalla-Dalla: Rukunin Mutane 3 da suka cancanci su sami bashi daga CBN na Kuɗin COVID19
Bayani Dalla-Dalla: Rukunin Mutane 3 da suka cancanci su sami bashi daga CBN na Kuɗin COVID19 Hoto: ciel.fr
Asali: UGC

CBN ya ware maƙudan kuɗaɗe kimanin 50 biliyan domin ƙunshin da farko, wanda bankin Microfinance ya rabawa yan Najeriya.

Rukunin yan Najeriya uku da suka cancanta su nemi rancen:

1. Magidanta

A jawabin bankin Microfinance, Magidanta yan Najeriya da suke da ƙwaƙƙwarar hujjar da zata nuna annobar ta shafi rayuwarsu, sun cancanci su nemi rancen.

KARANTA ANAN: Lokaci ya yi da zamu koma ga Allah, Mu baiwa Talakawa saɗaƙa a watan Ramadana, Inji Atiku

2. Masana'antu.

Hakanan, masan'antun Najeriya suna da damar neman rancen amma sai suna da shaidar da aka amince da ita a hukumance da zasu nuna cewa annobar ta shafi ayyukan masana'antun su.

3. Ƙanana da matsakaitan masana'antu.

Ƙanana da matsakaitan masana'antu dake da tsari da banki suna da damar da zasu yi amfani da ita wajen neman rancen TCF ɗin.

Kamar yadda bankin Micrifinance ya bayyana, yan Najeriya ka iya amfana da kimanin 25 miliyan daga farkon ƙunshin.

A wani labarin kuma Dalilin da yasa Sheikh Isa Pantami ya yi Muƙabala da Tsohon shugaban Boko Haram

Ɗaya daga cikin lauyoyin Ministan sadarwa, Sheikh Isa Pantami, ya bayyana dalilin da yasa ministan ya yi muƙabala da tsohon shugaban Boko Haram , Muhammad Yusuf.

Lauyan ya ce Pantami ya yi muƙabalar ne don ya ƙalubalanci irin koyarwar da Yusuf ɗin ke yi domin ta saɓa da koyarwar addinin musulunci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel