Lokaci ya yi da zamu koma ga Allah, Mu baiwa Talakawa saɗaƙa a watan Ramadana, Inji Atiku
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar PDP a zaɓen 2019 da ya gabata, Atiku Abubakar, ya taya musulman Najeriya murnan zagayowar watan azumin Ramadana
- Atiku ya ce wannan lokaci ne da kowa zai koma ga Allah ya roƙi dukkan buƙatunsa, kuma yace wannan lokaci ne da ya kamata masu kuɗi su bada sadaƙa
- A jiya dai Sarkin Musulmai ya bayarda sanarwar ganin jinjirin watan Ramadan a wasu sassan ƙasar nan, ya kuma umarci musulmai su ɗauki azumin farko yau Talata
Tshohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa lokacin azumin watan Ramadana shine lokacin da yafi da cewa kowa ya koma ga Allah.
KARANTA ANAN: Dalilin da yasa Sheikh Isa Pantami ya yi Muƙabala da Tsohon shugaban Boko Haram - Lauya
Atiku ya ce wannan ne lokacin da yafi da cewa mu maida hankali kan gina al'ummar mu kuma mu bayarda sadaƙa musamman ga mabuƙata.
Tsohon mataimakin shugaban ya yi wannan jawabi ne a wasu jerin saƙonni da ya fitar a dandalinsa na shafin tuwita don taya al'ummar musulmi barka da shigowar watan azumi.
Tsohon shugaban ya ce:
"Ina taya musulman Najeriya da ɗaukacin musulman duniya murna bisa sake ganin watan azumin Ramadana na wannan shekarar."
"Wannan shine lokacin da ya kamata mu maida hankali wajen gina jama'ar mu ta hanyar bayar da sadaƙa musamman ga waɗanda suke cikin tsantsar buƙatar taimako."
KARANTA ANAN: Najeriya na cikin tsaka mai wuya, Muna Buƙatar Addu'a, Inji gwamnan Lagos
"Kuma lokaci ne da ya kamata mu rungumi zaman lafiya, mu yi aiki tuƙuru domin cimma muradan mu da muka sa a gaba a karan kanmu da kuma jama'ar mu."
Tsohon mataimakin shugaban ya kuma roƙi mabiya addinin musulunci da su yi amfani da wannan damar guda ɗaya a shekara, su yi aikin dazai kai su kusa da Ubangijinsu.
Atiku ya ƙara da cewa, wannan dama ce da musulmai suka samu wajen roƙon Allah ya tausaya ya kawo sauki a cikin matsalolin da ƙasar nan ke fuskanta.
A wani labarin kuma Babu abinda da zai hana ni rufe duk Layukan da ba'a haɗa su da NIN ba, Sheikh Pantami
Ministan Sadarwar ƙasar nan, Isa Pantami,ya ƙara jaddada matsayarsa kan kulle duk wani layin waya da ba'a haɗa shi da NIN ba
Ministan ya faɗi haka ne a wani jerin saƙonni da ya fitar a shafin sa na Tuwita ya yin da yake martani kan wani labarin ƙanzon kurege da ake jingina mishi.
Asali: Legit.ng